1 Sai Yesu, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dawo daga kogin Urdun, sai Ruhu Mai Tsarki ya bishe shi zuwa cikin jeji 2 kwana arba'in, shaidan kuma ya jarabce shi. A kwanakin nan, bai ci abinci ba, kuma yunwa ta kama shi bayan karshen lokacin. 3 Shaidan ya ce masa, “Idan kai Dan Allah ne, ka umarci wannan dutse ya zama gurasa.” 4 Yesu ya amsa masa, “A rubuce yake, 'Ba da gurasa kadai Mutum zai rayu ba.'” 5 Sai shaidan ya kai shi zuwa wani tudu mai tsawo, ya kuma nuna masa dukan mulkokin duniyan nan a dan lokaci. 6 Shaidan ya ce masa, “Zan ba ka iko ka yi mulkin dukan wadannan, da dukan daukakarsu. Zan yi haka domin an ba ni su duka in yi mulkinsu, kuma ina da yanci in ba dukan wanda na ga dama. 7 Saboda da haka, idan ka rusuna ka yi mani sujada, dukansu za su zama naka.” 8 Amma Yesu ya amsa ya ce masa, “A rubuce yake, 'Dole ne Ubangiji Allahnka za ka yi wa sujada, shi kadai kuma za ka bauta wa.” 9 Sai shaidan ya kai Yesu Urushalima, ya tsayadda shi a bisan kololuwar haikali, kuma ya ce masa, “Idan kai Dan Allah ne, ka jefas da kanka kasa daga nan. 10 Domin a rubuce yake, 'Zai ba mala'ikunsa umarni su kiyaye ka, su kuma tsare ka,' 11 kuma, 'Za su daga ka sama a hannunsu, don kada ka yi tuntube a kan dutse.” 12 Yesu ya amsa masa cewa, “An fadi, 'Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.'” 13 Da shaidan ya gama yi wa Yesu gwaji, sai ya kyale shi sai wani lokaci. 14 Sai Yesu ya koma Galili cike da ikon Ruhu, kuma labarinsa ya bazu cikin dukan wuraren dake wannan yankin. 15 Ya yi ta koyarwa a cikin majami'unsu, sai kowa na ta yabon sa. 16 Wata rana ya zo Nazarat, birnin da aka rene shi. Kamar yadda ya saba yi, ya shiga cikin majami'a a nan ranar Asabaci, ya kuma tashi tsaye domin ya karanta Nassi. 17 An mika masa littafin anabi Ishaya, ya bude littafin ya kuma ga inda an rubuta, 18 “Ruhun Ubangiji yana kai na, domin ya shafe ni in yi wa'azin Bishara ga matalauta. Ya aike ni in yi shelar yanci ga daurarru, da kuma budewar idanu ga makafi, in 'yantar da wadanda su ke cikin kunci, 19 in kuma yi shelar shekarar tagomashi na Ubangiji.” 20 Sai ya rufe littafin, ya mai da shi ga ma'aikacin majami'ar, sai ya zauna. Dukan wadanda suke cikin majami'ar suka zura Idanuwansu a kansa. 21 Sai ya fara masu magana, “Yau wannan Nassi ya cika a kunuwanku.” 22 Dukan wadanda ke wurin sun shaida abin da ya fadi kuma dukansu sun yi ta mamakin kalmomin alheri da suke fitowa daga bakinsa. Suna cewa, “Wannan ai dan Yusufu ne kawai, ko ba haka ba?” 23 Yesu ya ce masu, “Lallai za ku fada mani wannan karin magana, 'Likita, ka warkar da kanka. Duk abin da mun ji wai ka yi a Kafarnahum, ka yi shi a nan garinka ma.'” 24 Ya sake cewa, “Hakika na fada maku, annabi baya samun karbuwa a garinsa. 25 Amma na gaya maku gaskiya akwai gwauraye da yawa cikin Isra'ila a zamanin Iliya, lokacin da an rufe sammai shekaru uku da rabi babu ruwa, lokacin da anyi gagarumar yunwa a duk fadin kasar. 26 Amma ba a aiki Iliya zuwa wurin waninsu ba, sai wurin gwauruwa da ke a Zarifat can kusa da Sidon. 27 Akwai kutare da yawa kuma a Isa'ila a zamanin anabi Elisha, amma babu wanda aka warkar sai dai Na'aman mutumin Suriya kadai. 28 Dukan mutanen da ke cikin majami'a suka fusata kwarai sa'adda suka ji wadannan zantattuka. 29 Suka tashi suka tura shi zuwa wajen birnin, suka kai shi bakin dutsen da aka gina garinsu a kai dominsu jefar da shi kasa. 30 Amma ya ratsa tsakaninsu ya yi gabansa. 31 Sannan ya gangara zuwa Kafarnahum, wani birni a Galili. Wata Asabaci yana koya wa mutane a cikin majami'a. 32 Sun yi mamaki kwarai da koyarwan sa, domin maganarsa na da iko. 33 A wannan lokacin akwai wani mutum a cikin majami'a mai kazamin ruhu, sai ya yi kara da babbar murya, 34 “Ina ruwan mu da kai, Yesu Banazarat? Ka zo domin ka hallaka mu ne? Na san ko kai wanene! Kai ne Mai Tsarki na Allah!” 35 Yesu ya tsauta wa aljanin yana cewa, “Yi shiru ka fita daga cikinsa!” Da aljanin ya jefar da mutumin kasa a tsakiyarsu, ya fita daga cikinsa ba tare da yi masa rauni ba. 36 Dukan mutanen suka yi mamaki, kuma suna ta zancen wannan abu a tsakaninsu. Sun ce, “Wanda irin maganganu kenan? Ya umarce kazaman ruhohin da karfi da iko kuma sun fita.” 37 Saboda da haka, an fara yada labarinsa zuwa dukan kewayen yankin. 38 Sai Yesu ya bar majami'ar ya shiga gidan Siman. A wannan lokacin, surukar Siman tana fama da zazzabi mai zafi, sai suka roke shi dominta. 39 Sai ya tsaya a kanta, ya tsautawa zazzabin, kuma ya rabu da ita. Nan take, ta tashi ta fara yi masu hidima. 40 Da faduwar rana, mutane suka kawo wa Yesu dukan wadanda suke ciwo da cuttuttuka dabam dabam. Ya dora masu hannuwansa ya warkar da su. 41 Aljanu kuma sun fita daga wadasunsu da dama, suna kuka cewa, “Kai ne Dan Allah!” Yesu ya tsauta wa aljannun ya kuma hana su magana, domin sun sani cewa shine Almasihu. 42 Da safiya ta yi, ya kebe kansa zuwa wani wurin da babu kowa. Jama'a da dama suna neman sa suka zo inda yake. Sun yi kokari su hana shi barin su. 43 Amma ya ce masu, “Dole in yi bisharar Allah a wasu birane da dama, domin dalilin da aka aiko ni nan kenan.” 44 Sai ya ci gaba da wa'azi cikin majami'u dukan fadin Yahudiya.
<- Luka 3Luka 5 ->