12
1 Da jimawa kadan, bayan da mutane da yawa suka taru kwarai har suna tattaka junansu. Sai ya fara yin magana da almajiransa. “Ku yi lura da yisti na Farisawa, wanda shine manufunci. 2 Amma ba abin da ke rufe wanda ba za a tone ba, ba kuma abin da ke boye wanda ba za a sani ba. 3 Saboda haka ba abin da za ku fadi a asirce wanda ba za a ji shi a cikin sarari ba. Abin da ku ka fadi da rada cikin lungu, za a yi shelarsa a ko'ina. 4 Ina gaya maku abokaina, kada ku ji tsoron wanda da za su kashe jiki. Bayan haka kuma ba abin da za su iya yi. 5 Bari in gargade ku a kan wanda za ku ji tsoronsa. Ku ji tsoron shi wanda bayan ya kashe zai iya jefa ku cikin jahannama. I, ina ce maku ku ji tsoronsa. 6 Ba a kan sayar da 'yan tsuntsaye biyar a kan anini biyu ba? Duk da haka, Allah ba zai manta da ko daya daga cikinsu ba. 7 Har ma gashin da ke kan ku ya san yawan su. Kada ku ji tsoro, ku kun fi tsuntsaye daraja a wurinsa. 8 Ina gaya maku, dukan wanda za ya shaida ni a gaban mutane, Dan Mutum kuma za ya shaida shi a gaban mala'kun Allah. 9 Kuma dukan wanda ya ki ni a gaban mutane, za a ki shi a gaban mala'ikun Allah. 10 Dukan wanda ya yi magana gaba da Dan Mutum, za a gafarta masa. Amma shi wanda ya yi sabon Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba. 11 Idan suka kawo ku gaban majami'a, ko gaban masu shari'a, ko gaban masu iko, kada ku damu da abin da za ku fada domin ku kare kanku. Ko kuwa abin da za ku ce. 12 Gama Ruhu Mai Tsarki zai koya maku abin da za ku fadi a wannan lokaci.” 13 Sai wani a cikin taron ya ce masa, “Malam, ka yi wa dan'uwana magana ya raba gado da ni 14 Yesu ya ce masa, “Kai, wanene ya sa ni in zama alkali, ko matsakanci a kanku?” 15 Sai kuma ya ce masu, “Ku yi lura kada ku zama masu hadama, gama ba abin da mutum ya mallaka ne ya fi mahimmanci a cikin rayuwar sa ba.” 16 Sa'annan Yesu ya fada masu wani misali, ya ce, “Gonar wani mutum ta bada amfani sosai, 17 ya yi tunani, ya ce, 'Me zan yi, domin ba ni da wurin da zan iya ajjiye amfanin gonata?' 18 Sai ya ce, na san abin da zan yi. Zan rushe rumbuna na in gina wadansu manya-manya, a nan zan ajjiye hatsi na da dukan abubuwa. 19 Sai in ce da raina, “Ya raina, kana da abu da yawa da aka ajjiye dominka, sai ka huta, ka ci, ka sha, ka yi murna.” 20 Amma sai Allah ya ce da shi, 'Wawan mutum, a cikin daren nan ana son ranka daga wurinka. Kayan da ka tara ka shirya wa kanka, na wa za su zama?' 21 Haka wanda ya tara wa kansa dukiya yake, idan ba shi da dukiya a wurin Allah.” 22 Yesu, ya ce da almajiransa, “Saboda haka ina cewa da ku, kada ku damu da rayuwarku, wato, abin da za ku ci, ko abin da za ku sa a jikinku. 23 Gama rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi. 24 Ku dubi hankaki wadanda ba sa yin shuka, ba sa yin girbi. Ba su da rumbuna ko dakunan ajjiya, amma Allah ya na ciyar da su. Ku fa kun fi tsuntsaye daraja! 25 Wanene a cikinku ta wurin sha'awarsa za ya iya karawa kansa kwanaki? 26 Idan ba ku iya yi wa kanku dan karamin abu ba, me ya sa za ku damu da sauran abubuwa? 27 Ku dubi furanni a daji - yadda suke yin girma. Ba su kan yi aiki ba, ba su kan yi kadi ba. Ina gaya maku, ko Sulaimanu, a cikin darajarsa, bai sa tufafin da suka fi nasu kyau ba. 28 Idan Allah ya sa wa ciyawa tufafi masu kyau haka, wadda yau tana nan, gobe kuma a sa ta a wuta, ta yaya zai kasa sa maku tufafi, ku masu kankantar bangaskiya! 29 Kada ku damu da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kuma kada ku yi alhini. 30 Gama dukan al'umman duniya suna neman wadannan abubuwa, kuma Ubanku ya san kuna bukatar wada nan abubuwan. 31 Amma ku bidi mulkinsa, wadannan abubuwa kuma za a kara maku su. 32 Kada ku ji tsoro, ku 'yan kanana, domin da murna Ubanku zai ba ku mulkin. 33 Ku sayar da abin da ku ke da shi ku ba matalauta. Kuyi wa kanku jakukkuna wadanda ba za su lalace ba, ku yi ajjiya cikin sama inda abin ba ya karewa, inda barayi ba za su iya zuwa ba, kwari kuma ba za su iya lalatawa ba. 34 Domin inda dukiyarka take, can zuciyarka za ta kasance kuma. 35 Ku rage tsawon tufafinku, ku yi dammara, ya zama fitilarku tana ci koyaushe, 36 ku kuma zama kamar wadanda suke jiran mai gidansu ya dawo daga gidan buki, domin duk sa'adda ya zo ya kwankwasa kofa, nan da nan za su bude masa. 37 Masu albarka ne wadannan bayi, wadanda ubangijinsu za ya tarar suna jiran dawowar sa. Gaskiya ni ke gaya ma ku, zai yi dammara yasa su zazzauna ya ba su abinci shi da kansa. 38 Ko da ubangijinsu ya zo da dare, ko da tsakar dare, ya tarar da su a shirye suna jiransa. Masu albarka ne wadannan bayi. 39 Kuma ku san wannan, da mai gida ya san lokacin da barawo zai zo, ba zai bari a fasa masa gida a shiga ba. 40 Sai ku zauna da shiri fa domin ba ku san lokacin da Dan Mutum zai dawo ba.” 41 Sai Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, mu ka ke fadawa wannan misali, ko ga kowa da kowa ne?” 42 Sai Ubangiji ya ce, “Wanne shugaba ne, mai aminci, mai hikima kuma wanda ubangijinsa za ya damka bayinsa a hannunsa, domin ya kula da su, ya ba su abincinsu a kan lokaci? 43 Mai albarka ne wannan bawa, wanda ubangijinsa za ya tarar da shi yana yin abin da aka sa shi ya yi. 44 Hakika, ina gaya maku, zai danka dukan malakarsa a gareshi. 45 Amma idan wannan bawa, ya ce a cikin zuciyarsa, 'Ubangiji na yayi jinkirin dawowa,' sai ya fara dukan bayin, maza da mata abokan bautarsa, ya ci ya sha, ya bugu, 46 ubangijin bawan nan zai dawo a lokacin da bawan bai sa tsammani ba, kuma a cikin lokacin da bai sani ba, ya daddatsa shi gunduwa-gunduwa, ya kuma hada shi da marasa aminci. 47 Bawan nan, ya san halin ubagijinsa, amma bai shirya yayi abin da ubangijinsa yake so ba. Zai sha duka da bulala da yawa. 48 Amma shi wanda bai sani ba, kuma yayi abin da ba daidai ba, ba zai sha duka da bulala da yawa ba. Dukan wanda aka ba abu da yawa, za a kuma nemi abu da yawa daga wurinsa. Kuma ga wanda aka ba abu da yawa amana, za a nemi abu mafi yawa daga gareshi. 49 Na zo domin in sa wuta a duniya, na so da ta riga ta kama. 50 Amma ni, ina da baftisma wadda za a yi mani baftisma da ita, kuma na kagara, da an riga an yi ta! 51 Kuna zaton na zo duniya domin in kawo salama? Na ce maku a'a, amma tsattsaguwa. 52 Daga yanzu za a sami mutane biyar a cikin gida daya, kuma za su rarrabu, mutane uku suna gaba da biyu, biyun kuma suna gaba da ukun. 53 Da da mahaifi za su yi gaba da juna, dan zai yi gaba da mahaifinsa. Mahaifiya za ta yi gaba da diyarta, diya kuma gaba da mahafiyarta; uwar miji za ta yi gaba da matar danta, matar da kuma gaba da uwar mijinta.” 54 Yesu, ya kuma gaya wa taron, “Da kun ga hadari ya taso daga yamma, nan da nan sai ku ce za a yi ruwa, haka kuwa ya kan zama. 55 Idan iska tana busowa daga kudu sai ku ce za a yi zafi mai tsanani, haka kuwa ya kan faru. 56 Munafukai, kun iya fasarta yanayin kasa da sama, amma baku iya fasarta abin da yake faruwa yanzu ba? 57 Me ya sa ba ku iya gane abin da zai tamake ku? 58 Idan kuna tafiya wurin shari'a da abokin husumarka, ka yi kokari ku daidaita tun a kan hanya domin kada ya kai ka wurin mai shari'a. Domin kada mai shari'a ya mika ka ga mai tsaron kurkuku, shi kuwa mai tsaron kurkuku ba zai nuna maka sani a cikin kurkuku ba. 59 Na gaya maka, ba za ka iya fitowa ba sai ka biya dukan kudin da a ke binka?
<- Luka 11Luka 13 ->
Luka