Link to home pageLanguagesLink to all Bible versions on this site
11
1 Wani lokaci, Yesu yana yin addu'a a wani wuri, sai daya daga cikin almajiransa yace da shi, “Ubangiji, ka koya mana yin addu'a kamar yadda Yahaya ya koya wa almajiransa.” 2 Yesu ya ce ma su, “Sa'anda ku ke yin addu'a ku ce, 'Uba a tsarkake sunanka. Mulkin ka ya zo. 3 Ka ba mu abin da za mu ci a kowacce rana. 4 Gafarta mana zunubanmu, kamar yadda muke gafarta ma wadanda suke mana laifi. Kada ka kai mu cikin jaraba.'” 5 Yesu ya ce masu, “Wanene a cikinku idan yana da aboki, za ya je wurinsa da tsakar dare ya ce masa, ''Aboki, ka ba ni rancen dunkulen gurasa guda uku, 6 da ya ke wani abokina ya iso yanzu daga tafiya, kuma ba ni da abin da zan ba shi ya ci,' 7 Sai wanda yake ciki, ya amsa, ya ce, 'Kada ka dame ni. Na riga na rufe kofa ta, kuma ni da yarana mun riga mun kwanta. Ba zan iya tashi in ba ka gurasa ba.' 8 Na fada maku, ko da bai tashi ya ba ka gurasar ba, a matsayin abokinsa, ba ka ji kunya ba, ka nace da rokonsa, za ya tashi ya ba ka dukan yawan gurasar da kake bukata. 9 Ni kuma ina ce maku, ku roka za a ba ku; ku nema za ku samu; ku kwankwasa za a bude maku. 10 Domin dukan wanda yake roko ya na karba; dukan wanda ya ke nema kuma yana samu; kuma wanda yake kwankwasawa, za a bude masa. 11 Wanne uba ne a cikinku, idan dansa ya tambaye shi kifi, zai ba shi maciji a maimakon kifi? 12 Ko kuwa idan ya tambaye shi kwai, za ya ba shi kunama? 13 To, da yake ku da kuke masu mugunta kun san ku ba 'yanyan ku abu mai kyau. Yaya fa ga Ubanku wanda yake cikin sama, za ya ba da Ruhu Mai Tsarki ga wadanda suka roke shi?” 14 Wani lokaci, Yesu yana fitar da wani beben aljani. Sa'adda aljanin ya fita, sai mutumin da yake bebe ya yi magana. Sai taron mutanen suka yi mamaki! 15 Amma, wadansu daga cikin mutanen suka ce, “Da ikon Ba'alzabuba sarkin aljanu ne yake fitar da aljanu.” 16 Wadansu suka gwada shi, suka nemi ya nuna masu wata alama daga sama. 17 Amma Yesu da yake ya san tunaninsu, ya ce da su, “Dukan mulkin da ya rabu biyu, gaba da kansa, ya rushe kenan, kuma idan gida ya rabu biyu, gaba da kansa za ya fadi. 18 Idan Shaidan ya rabu biyu gaba da kansa, ta yaya mulkinsa zai iya tsayawa? Gama kun ce ina fitar da aljanu ta wurin Ba'alzabuba. 19 Idan ni na fitar da aljanu ta wurin Ba'alzabuba, ta wurin wa wadanda suke bin ku suke fitar da aljanu? Saboda haka, su ne zasu zama masu yi maku shari'a. 20 Amma idan daga wurin Allah na ke fitar da aljanu, to, ya zama ke nan mulkin Allah ya zo wurinku. 21 Idan mutum mai karfi, mai kayan fada ya tsare gidansa, kayansa za su tsira. 22 Amma idan wani mutum wanda ya fi shi karfi ya zo ya ci nasara a kansa, zai dauke kayan fadan daga wurin mutumin, kuma ya kwashe kayansa. 23 Wanda ba ya tare da ni, gaba da ni ya ke yi, kuma wanda ba ya tattarawa tare da ni, watsarwa yake yi. 24 Idan kazamin ruhu ya fita daga cikin mutum, ya kan bi ta wurin busassun wurare yana neman wurin da zai huta. Idan bai samu ba sai ya ce, 'Bari in koma gidana inda na baro. 25 Sa'adda ya dawo, ya tarar an share gidan, an kuma gyara shi tsaf. 26 Sai ya je ya dauko wadansu aljanu guda bakwai wadanda su ka fi shi mugunta, su zo su zauna a wurin. Sai karshen mutumin nan ya fi farkonsa muni.” 27 Ya zama, lokacin da ya ke fadin wadannan abubuwa, wata mace ta tada muryarta a cikin taron mutanen ta ce da shi, “Mai albarka ne cikin da ya haife ka, da maman da ka sha.” 28 Sai shi kuma ya ce, “Masu albarka ne wadanda suke jin maganar Allah suke yin biyayya da ita.” 29 Lokacin da mutane suke kara taruwa, sai ya fara cewa, “Wannan tsara, muguwar tsara ce. Ta na neman alama, Ko da yake ba wata alamar da za a bata sai irin ta Yunusa. 30 Domin kamar yadda Yunusa ya zama alama ga mutanen Neneba, haka kuma Dan Mutum za ya zama alama ga wannan tsara. 31 Sarauniyar Kudu, za ta tsaya ta yi shari'a da mutanen wannan tsara, kuma za ta kashe su, gama ta zo daga wuri mai nisa domin ta saurari hikimar Sulaimanu. Kuma ga wani wanda ya fi Sulaimanu a nan. 32 Mutanen Neneba, za su tsaya shari'a da matanen wannan tsara, kuma za su kashe su. Gama sun ji wa'azin Yunusa sun tuba. Kuma ga wani wanda ya fi Yunusa a nan. 33 Ba wanda zai kunna fitila ya boye ta, ko kuwa ya sa ta a karkashin kasko, amma zai sa ta a mazaunin ta domin dukan wanda ya shiga dakin ya ga haske. 34 Idon ku shine fitilar jikinku. Idan idonku yana gani sosai, jikinku zai cika da haske. Amma idan idonku ba ya gani sosai, jikinku zai cika da duhu. 35 Ku yi hankali fa, domin kada hasken da ya ke wurinku ya zama duhu. 36 Idan dukan jikinku yana cike da haske, babu duhu ko kadan, to sai dukan jikinku ya zama kamar fitilar da take bada haskenta a bisanku.” 37 Sa'adda ya gama jawabi, sai wani Bafarise ya ce da shi ya zo gidansa ya ci abinci, sai Yesu ya shiga ya zauna. 38 Sai Bafarisen ya yi mamaki da ganin bai wanke hannu kafin ya ci abinci ba. 39 Amma sai Ubangiji ya ce da shi, “Ku Farisawa kuna tsabtace bayan kofi da bangaji, amma cikin yana cike da kazamta da mugunta. 40 Ku mutane marasa tunani, wanda ya yi wajen, ba shine ya yi cikin ba? 41 Ku bayar da abin da ke ciki ga matalauta, kuma dukan abu zai zamar maku da tsafta. 42 Amma kaitonku Farisawa, gama kuna karbar zakka da daddoya da karkashi da kowanne irin ganye na lambu, amma kun watsar da adalci da kaunar Allah. Dole ne a yi adalci, a kaunaci Allah, a yi sauran abubuwan kuma. 43 Kaitonku Farisawa, domin kuna so a ba ku wuraren zama masu kyau a cikin masujadai, a kuma yi maku gaisuwar bangirma a cikin kasuwanni. 44 Kaiton ku, gama kuna kama da kabarbarun da ba yi masu shaida ba, mutane kuwa suna tafiya akansu ba tare da saninsu ba.” 45 Wani malami a cikin shari'ar Yahudawa ya amsa masa ya ce, “Malam, abin da ka ce ya bata mana rai mu ma.” 46 Sai Yesu ya ce, “Kaitonku malaman shari'a! Gama kun dora wa mutane kaya mai nauyi wanda ya fi karfinsu dauka. Amma ku, ko da dan yatsa ba ku taba kayan ba. 47 Kaiton ku, gama kuna gina abubuwan tunawa a kabuburan annabawa, alhali kuwa kakanni-kakanninku ne suka kashe su. 48 Ya zama kenan kuna sane da ayyukan kakanni-kakanninku, domin sune suka kashe annabawan da kuke tunawa da su. 49 Saboda wannan daliline hikimar Allah ta ce, ''Zan aika manzanni da annabawa a wurinsu, kuma za su tsananta masu har ma za su kashe wadansu daga cikinsu.' 50 Wannan tsarar, za ta dauki alhakin jinin dukan annabawan da aka kashe tun kafuwar duniya. 51 Tun daga jinin Habila, har zuwa jinin Zakariya wanda aka kashe tsakanin bagadi da wuri mai tsarki. I, na gaya ma ku za a nemi hakin su a wurin wannan tsarar 52 Kaitonku malaman shari'a na Yahudawa, domin kun dauke mabudin sani, ku da kanku ba ku shiga ba, kuma kun hana masu shiga su shiga.” 53 Bayan da Yesu ya bar nan wurin, Marubuta da Farisawa suka yi gaba da shi, suka yi jayayya da shi a kan abubuwa da yawa, 54 suna kokari su kafa masa tarko domin su kama shi a cikin kalmomin da yake fadi.

<- Luka 10Luka 12 ->
  • Luka