1 Da Yesu ya sani cewa Farisawa sun ji cewa yana samun almajirai yana kuma yi masu baftisma fiye da Yahaya 2 (ko da shike ba Yesu da kansa ke yin baftismar ba, amma almajiransa ne), 3 ya bar Yahudiya ya koma Galili. 4 Amma ya zamar masa dole ya ratsa ta Samariya. 5 Ya zo wani birnin Samariya, mai suna Sika, kusa da filin da Yakubu ya ba dansa Yusufu. 6 Rijiyar Yakubu na wurin. Da Yesu ya gaji da tafiyarsa sai ya zauna gefen rijiyar. Kusan karfe goma sha biyu na rana ne. 7 Wata mace, Ba-Samariya ta zo domin ta dibi ruwa, sai Yesu ya ce mata, “Ba ni ruwa in sha.” 8 Gama almajiransa sun tafi cikin gari don sayen abinci. 9 Sai ba-Samariyar tace masa, “Yaya kai da kake Bayahude kake tambaya ta ruwan sha, ni da nike 'yar Samariya?” Domin Yahudawa ba su harka da Samariyawa. 10 Sai Yesu ya amsa yace mata, “In da kin san kyautar Allah, da shi wanda yake ce da ke, 'Ba ni ruwan sha,' da kin roke shi, sai kuma ya ba ki ruwan rai.” 11 Matar tace masa, “Mallam, ga shi ba ka da guga, kuma rijiyar tana da zurfi. Ina za ka samu ruwan rai? 12 Ai ba ka fi Ubanmu Yakubu ba, ko ka fi shi, shi wanda ya ba mu rijiyar, shi kansa kuma ya sha daga cikin ta, haka kuma 'ya'yansa da shanunsa?” 13 Yesu ya amsa yace mata, “duk wanda ya sha daga wannan ruwan zai sake jin kishi, 14 amma duk wanda ya sha daga ruwa da zan ba shi ba zai sake jin kishi ba. Maimakon haka, ruwan da zan bashi zai zama mabulbular ruwa a cikinsa wanda ke bulbula zuwa rai madawwami.” 15 Matar tace masa, “Mallam, ka ba ni wannan ruwa yadda ba zan kara jin kishi ba ba kuma sai na zo nan don in dibi ruwa ba.” 16 Yesu ya ce mata, “Je, ki kira maigidanki ku zo nan tare.” 17 Matar ta amsa tace masa, “Ba ni da miji.” Yesu yace, “Kin fadi daidai da kika ce, 'ba ni da miji,' 18 domin kin auri mazaje har biyar, kuma wanda kike da shi yanzu ba mijin ki bane. Abinda kika fada gaskiya ne.” 19 Matar tace masa, “Mallam, Na ga kai annabi ne. 20 Ubaninmu sun yi sujada a wannan dutse, amma kun ce Urushalima ce wurin da ya kamata mutane su yi sujada.” 21 Yesu ya ce mata, “Mace, ki gaskata ni, cewa lokaci na zuwa wanda ba za ku yi wa Uban sujada ba ko akan wannan dutse ko a Urushalima. 22 Ku kuna bauta wa abinda ba ku sani ba. Mu muna bauta wa abinda muka sani, gama ceto daga Yahudawa yake. 23 Sai dai, sa'a tana zuwa, har ma ta yi, wadda masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a cikin ruhu da gaskiya, domin irin wadannan ne Uban ke nema su zama masu yi masa sujada. 24 Allah Ruhu ne, kuma mutanen da ke yi masa sujada, dole su yi sujada cikin ruhu da gaskiya.” 25 Matar ta ce masa, “Na san Almasihu na zuwa (wanda ake kira Kristi). Sa'adda ya zo, zai bayyana mana kowane abu. 26 Yesu ya ce mata, “Ni ne shi, wanda ke yi maki magana.” 27 A daidai wannan lokaci, almajiransa suka dawo. Suna ta mamakin dalilin da yasa yake magana da mace, amma babu wanda yace, “Me kake so?” Ko kuma, “Don me ka ke magana da ita?” 28 Sai matar ta bar tulunta, ta koma cikin gari, tace wa mutanen, 29 “Ku zo ku ga wani mutum wanda ya gaya mani duk wani abu da na taba yi. Wannan dai ba Almasihun bane, ko kuwa?” 30 Suka bar garin suka zo wurinsa. 31 A wannan lokacin, almajiransa suna rokansa, cewa, “Mallam, ka ci.” 32 Amma ya ce masu, “ina da abinci da ba ku san komai akai ba.” 33 Sai almajiran suka ce da junansu, “Babu wanda ya kawo masa wani abu ya ci, ko akwai ne?” 34 Yesu ya ce masu, “Abincina shine in yi nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa. 35 Ba ku kan ce, 'akwai wata hudu tukuna kafin girbi ya zo ba?' Ina gaya maku, daga idanunku ku ga gonakin, sun rigaya sun isa girbi. 36 Shi wanda ke girbi yakan karbi sakamako ya kuma tattara amfanin gona zuwa rai na har abada, ta haka shi mai shuka da shi mai girbi za su yi farinciki tare. 37 Gama cikin wannan maganar take, 'Wani na shuka, wani kuma na girbi.' 38 Na aike ku ku yi girbin abinda ba ku yi aiki a kai ba. Wandansu sun yi aiki, ku kuma kun shiga cikin wahalarsu. 39 Yawancin Samariyawan da ke wannan birni suka gaskata da shi sabili da labarin matar data bada shaida, “Ya gaya mani duk abinda na taba yi.” 40 To sa'adda Samariyawa suka zo wurinsa, sai suka roke shi ya zauna tare da su, ya kuwa zauna wurin kwana biyu. 41 Wasu da dama kuma suka gaskata domin maganarsa. 42 Suka cewa matar, “Mun bada gaskiya, ba saboda maganar ki kadai ba, amma mu kanmu munji, yanzu kuma mun sani cewa wannan lallai shine mai ceton duniya.” 43 Bayan wadannan kwana biyu, ya bar wurin zuwa Galili. 44 Domin Yesu da kansa yace, ba a girmama annabi a kasarsa. 45 Da ya zo Galili, Galiliyawan suka marabce shi. Sun ga dukan abubuwan da ya yi a Urushalima wurin idin, domin su ma sun je idin. 46 Kuma ya koma Kana ta Galili inda ya mayar da ruwa zuwa ruwan inabi. Akwai wani ma'aikacin fada wanda dansa na rashin lafiya a Kafarnahum. 47 Da ya ji cewa Yesu ya bar Yahudiya ya koma Galili, sai ya tafi wurin Yesu ya roke shi ya sauko ya warka da dansa wanda ke bakin mutuwa. 48 Yesu yace masa, “Idan ba ku ga alamu da mu'ujizai ba, ba za ku gaskata ba.” 49 Ma'aikacin ya ce masa, “Mallam, ka sauko kafin da na ya mutu.” 50 Yesu yace masa, “Je ka. Dan ka ya rayu.” Mutumin ya gaskata maganar da Yesu ya gaya masa, Sai yayi tafiyarsa. 51 Yayin da yake sauka kasa, bayinsa suka same shi, suna cewa, danka yana raye. 52 Sai ya tambaye su sa'ar da ya fara samun sauki. Suka amsa masa, “Jiya a sa'a ta bakwai zazabin ya bar shi.” 53 Sai Uban ya gane cewa wannan sa'a ce Yesu ya ce masa, “Jeka, danka na raye.” Sabili da haka, shi da dukan gidansa suka bada gaskiya. 54 Wannan ce alama ta biyu da Yesu ya yi bayan da ya bar Yahudiya zuwa Galili.
<- Yahaya 3Yahaya 5 ->