Link to home pageLanguagesLink to all Bible versions on this site
10
1 Domin shari'a hoto ce na kyawawan abubuwan da ke zuwa, ba ainihin siffar wadannan abubuwa ba. Wadanda ke gusowa kusa da Allah ba za su taba ingantuwa ta wurin hadayu da firistoci ke mikawa shekara da shekaru ba. 2 In ba haka ba, ba sai a dena mika hadayun ba? Bisa ga wannan al'amari, inda sun tsarkaka sau daya tak da masu sujada ba su san menene zunubi ba. 3 Amma wadannan hadayun sun zama matuni ne na zunubi shekara biye da shekara. 4 Domin ba shi yiwuwa jinin bijimai da awakai su kawar da zunubai. 5 Yayin da Almasihu ya zo duniya, ya ce, “Ba hadayu da sadakoki kake marmari ba. Maimakon haka, ka shirya mini jiki domin hadaya. 6 Baka murna domin sadakoki da hadayu na konawa domin zunubi. 7 Sai na ce, 'Duba, gani na zo in yi nufinka, kamar yadda aka rubuta akaina.''' 8 Da fari Yace ''ba hadayu, ko sadakoki, ko kuma hadaya ta konawa domin zunubi kake bukata ba. Ba ka kuwa jin dadinsu.'' Wadannan sune hadayun da ake bayarwa bisa ga shari'a. 9 Sa'annan sai ya ce ''gani na zo domin in aikata nufinka.” Ya kawar da hidimar farko domin ya kafa hidima ta biyu. 10 A hidima ta biyu, an kebe mu ga Allah ta wurin nufinsa ta wurin hadayar jikin Yesu Almasihu bugu daya ba kari. 11 Haka, kowanne firist ya ke tsayawa kulliyomi domin ya yi hidima ga Allah. A kullum yana mika hadayu, iri daya, koda shike ba za su taba kawar da zunubai ba. 12 A ta wata hanya kuma, Almasihu ya mika hadaya sau daya tak domin zunubai har abada, ya zauna a hannun dama na Allah. 13 Yana jiran har a maida makiyansa matashin sawayensa. 14 Domin ta wurin hadaya guda dayan nan ya kammala har abada ga wadanda suka sadaukar da kansu ga Allah. 15 Kuma Ruhu mai Tsarki ya shaida mana. Abu na farko yace, 16 “Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su a bayan kwanakin nan,' inji Ubangiji Zan sa dokokina a cikin zukatansu, kuma zan rubuta su a lamirinsu. 17 Ba zan sake tunawa da zunubansu da kurakuransu ba.'' 18 Yanzu fa duk in da aka sami gafara domin wadannan abubuwa, babu wata hadaya domin zunubi. 19 Saboda haka, yan'uwa, ba mu da shakkar shigowa wurin nan mafi tsarki ta wurin jinin Yesu. 20 Wannan ita ce sabuwar rayayyar hanya da ya bude mana ta wurin labulen, wato ta wurin jikinsa. 21 Saboda muna da babban firist a gidan Allah. 22 Bari mu matso kusa da sahihiyar zuciya, da kuma cikakken gabagadi cikin bangaskiya, da zuciyarmu wadda aka tsarkake daga mummunan tunani, da kuma jikunanmu wankakku da ruwa mai tsabta. 23 Bari mu rike da karfi shaidar bangaskiyar begenmu, ba tare da raurawa ba, domin Allahn, da ya yi alkawari, mai aminci ne. 24 Bari mu kuma yi lura yadda za mu iza juna ga kauna da ayyuka masu dacewa. 25 Kada mu fasa zumunci da juna, kamar yadda wadansu sukan yi. A maimakon haka, bari mu karfafa juna a kulluyomin, kamar yada kuke ganin kusantowar ranan nan. 26 Saboda idan mun ci gaba da zunubin ganganci bayan mun rigaya mun sami wannan sanin gaskiyar, hadayar irin wannan zunubi bata samuwa. 27 Maimakon haka, sai fargabar babban tsoron hukunci, da kuma wuta mai zafi, da zata cinye makiyan Allah. 28 Dukkan wanda ya ki bin dokar Musa zai mutu ba tausayi ta wurin shaidu biyu ko uku. 29 Wanne irin hukunci kuke tsammani ya dace ga wadanda suka raina Dan Allah, duk wadanda suka maida jinin alkawarin nan kamar ba tsarkakakke ba, wanda ta wurin jinin nan ne aka kebe shi ga Allah- wadanda suka wulakantar da Ruhun alheri? 30 Domin mun san wanda yace, “Ramako nawa ne; Zan yi sakayya.'' Sa'annan kuma, “Ubangiji zai hukumta jama'arsa.” 31 Abin tsoro ne a fada cikin hannuwan Allah mai rai! 32 Amma ku tuna da kwanakin baya, bayan da ku ka sami haske, yadda kuka jure babban fama cikin wahala. 33 Aka kunyatar da ku a gaban jama'a, ta wurin ba'a da cin mutunci, kuna kuma dandana irin azabar da wadansu suka shiga ciki. 34 Domin kuna da tausayi ga wadanda suke kurkuku, da farin ciki, kun amince da kwace na dukiyarku da aka yi, kun mallaki madauwamiyar mallaka mafi kyau. Dominn kun ji tausayina sa'adda na ke a kurkuku. 35 Don haka kada ku yarda gabagadinku, wanda ke da babban sakamako. 36 Domin kuna bukatar hakuri don ku sami abin da Allah ya alkawarta, bayan kun aikata nufinsa. 37 “Domin a dan karamin lokaci, mai zuwan nan zai zo ba zai yi jinkiri ba. 38 Adalina kuwa zai rayu ta wurin bangaskiya. In kuwa ya ja da baya, ba zan yi farin ciki dashi ba.” 39 Amma mu bama cikin wadanda suka ja da baya zuwa hallaka. Maimakon haka, muna cikin wadanda suke da bangaskiya domin kula da rayukanmu.

<- Ibraniyawa 9Ibraniyawa 11 ->
  • Ibraniyawa