1 Ku Galatiyawa marasa wayo! Wanne mugun ido ya cuce ku? Ashe, ba Yesu Almasihu gicciyayye aka nuna a gaban idon ku ba? 2 Ina so in gane wannan daga wurin ku ne kawai. Kun karbi Ruhun ta wurin ayyukan doka ne ko ta wurin ba da gaskiya ga abin da kuka ji? 3 Rashin wayonku ya yi yawa haka ne? Kun fara da Ruhu, sai kuma yanzu ku karasa a cikin jiki? 4 Kun fuskanci abubuwa da yawa a banza ne - har idan a banza ne? 5 To, shi wanda ya ba ku Ruhun, da ayyuka masu iko a tsakanin ku, ya yi ne ta wurin ayyukan shari'a ko ta wurin ji tare da bangaskiya? 6 Ibrahim ''ya ba da gaskiya ga Allah, kuma an lisafta mashi wannan a matsayin adalci.'' 7 Ta wannan hanya ku fahimta su wadanda suka ba da gaskiya, 'ya'yan Ibrahim ne. 8 Nassi ya riga ya hangi gaba cewa, ta wurin bangaskiya Allah zai baratar da Al'ummai. An yi wa Ibrahim shelar bishara tuntuni: ''A cikinka ne dukan al'ummai za su yi albarka.'' 9 Saboda haka, wadanda suka ba da gaskiya, masu albarka ne tare da Ibrahim wanda ke da bangaskiya. 10 La'ana na kan wadanda sun dangana ga ayyukan shari'a. Gama a rubuce yake, ''La'ananne ne kowanne mutum da bai tsaya ga duk abin da ke a rubuce cikin littafin shari'a ba, ya kuma aikata shi duka.”' 11 Yanzu a sarari yake, Allah ba ya baratar da kowa ta wurin shari'a, domin ''Mai adalci zai rayu ta bangaskiya.'' 12 Doka ba daga bangaskiya take ba, 'Amma a maimakon haka, “Shi wanda ke yin wadannan abubuwa cikin shari'a, zai yi rayuwa ta wurin shari'a.'' 13 Almasihu ya fanshe mu daga la'anar shari'a da ya zama la'ananne saboda mu. Kamar yadda yake a rubuce, ''La'ananne ne duk wanda aka sargafe a bisa itace.'' 14 Dalilin shine, albarkan da ke bisan Ibrahim ta zo ga al'ummai cikin Almasihu Yesu, domin mu samu karban alkawarin Ruhu ta wurin bangaskiya. 15 'Yan'uwa, ina magana bisa ga ka'idojin mutane. Idan mutane sun yi yarjejeniya, babu mai kawar da shi ko a kara shi. 16 Yanzu fa, an fada alkawaran nan ne ga Ibrahim da zuriyarsa. Bai ce, ''ga zuriya ba'' da manufar masu yawa; amma a maimakon haka ga daya kadai, ''ga zuriyar ka,'' wanda shine Almasihu. 17 Yanzu na fadi wannan. Shari'a, wadda ta zo shekaru 430 daga baya, ba ta kawar da alkawarin da Allah ya tabbatar da shi ba tun a baya. 18 Domin idan da gadon ya zo ta dalilin shari'a ne, da ba za ya zo kuma ta dalilin alkawari ba. Amma Allah ya ba da shi ga Ibrahim kyauta ta wurin alkawari. 19 Me ya sa kenan aka ba da shari'a? An kara ta ne saboda laifuffuka, har sai zuriyar Ibrahim din nan ta zo ga wadanda aka yi masu alkawarinta. An kaddamar da ikon shari'ar ta wurin mala'iku, ta hannun matsakaici. 20 Yanzu dai matsakanci yana nufin mutum fiye da daya, duk da haka Allah daya ne. 21 Shari'a tana tsayayya da alkawaran Allah kenan? Ko kadan! Domin idan da an ba da shari'a da ke iya bayar da rai, babu shakka da adalci ya zo ta wurin wannan shari'a. 22 A maimakon haka, nassi ya kulle abubuwa duka a karkashin zunubi. Allah ya yi wannan domin alkawarin sa na ceton mu ta wurin bangaskiya cikin Yesu Almasihu ya samu a ba da shi ga wadanda suka gaskanta. 23 Amma kafin bangaskiya cikin Almasihu ta zo, an kulle mu kuma aka tsare mu da shari'a har zuwa ga wahayin bangaskiya. 24 Daga nan shari'a ta zama mana jagora har sai da Almasihu ya zo, domin mu samu baratarwa ta wurin bangaskiya. 25 Yanzu da bangaskiya ta zo, ba mu kuma a karkashin jagora. 26 Domin dukanku 'ya'yan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Almasihu Yesu. 27 Dukanku da aka yi wa baftisma cikin Almasihu, kun suturce kanku da Almasihu. 28 Babu Bayahude ko Baheline, bawa ko 'yantacce, babu na miji ko mace, domin dukanku daya ne cikin Almasihu Yesu. 29 Idan ku na Almasihu ne, ku zuriyar Ibrahim ne kenan, magada bisa ga alkawarin.
<- GALATIYAWA 2GALATIYAWA 4 ->