2 Sai ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?”
3 Sai ya ce mini, “Wannan ce la’anar da za tă ratsa dukan ƙasar; gama bisa ga abin da ya ce a gefe ɗaya, za a kawar da kowane ɓarawo, kuma bisa ga abin da ya ce a ɗaya gefen za a kawar da duk mai rantsuwar ƙarya. 4 Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Zan aika shi, zai shiga gidan ɓarawo, da gidan mai rantsuwar ƙarya da sunana. Zai kasance a gidansa yă hallaka gidan da katakon da duwatsun.’ ”
6 Na tambaya na ce, “Mene ne?”
7 Sa’an nan aka ɗaga murfin dalman, a ciki kuwa ga mace zaune! 8 Ya ce, “Wannan mugunta ce,” ya kuma tura ta cikin kwandon ya rufe da murfin dalman, ya kuma danna da dutse.
9 Na ɗaga idona sama, sai ga mata biyu a gabana, iska tana hura fikafikansu! Suna da fikafikai kamar na shamuwa, suka kuma ɗaga kwandon sama.
10 Na tambayi mala’ikan da yake magana da ni na ce, “Ina za ku kai kwandon?”
11 Ya amsa ya ce, “Zuwa ƙasar Babiloniya[d] don a gina masa haikali. Sa’ad da aka gama ginin, za a ajiye shi a ciki.”
<- Zakariya 4Zakariya 6 ->- a Da Ibraniyanci tsawonsa kamu ashirin, fāɗinsa kuma kamu goma (tsawonsa wajen mita 9, fāɗinsa kuma wajen mita huɗu da rabi).
- b Da Ibraniyanci efa ne; haka ma a ayoyi 7-11.
- c ko kuwa bayyanuwar
- d Da Ibraniyanci Shinar. Shinar tsohon sunan Babilon ne. Bisa ga Far 11, a wurin ne mutanen dā suka gina gini mai tsayi na saɓo ga Allah, wanda Ubangiji ya sauka ya dagula harsunansu.