Zabura 89
Maskil*Kan magana, mai yiwuwa kalmar waƙa ce. na Etan dangin Ezra.
1 Zan rera game da ƙauna mai girma ta Ubangiji har abada;
da bakina zan sanar da amincinka
a dukan zamanai.
2 Zan furta cewa ƙaunarka tana nan daram har abada,
cewa ka kafa amincinka a sama kanta.
3 Ka ce, “Na yi alkawari da zaɓaɓɓena,
na rantse wa Dawuda bawana,
4 cewa ‘Zan kafa zuriyarka har abada
in kuma sa kursiyinka yă tsaya daram dukan zamanai.’ ”
Sela
5 Sammai na yabon abubuwan banmamakinka, ya Ubangiji,
amincinka shi ma, a cikin taron tsarkakanka.
6 Gama wane ne a sarari za a iya kwatanta da Ubangiji?
Wane ne yake kamar Ubangiji a cikin talikan samaniya?
7 Cikin taron tsarkaka Allah ne aka fi tsoro;
shi ne mafi bantsoro fiye da dukan waɗanda suka kewaye shi.
8 Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, wane ne kamar ka?
Kai mai iko ne, ya Ubangiji, kuma amincinka ya kewaye ka.
9 Kana mulkin teku mai tumbatsa;
sa’ad da raƙuma sun tashi, kakan kwantar da su.
10 Ka ragargaza Rahab kamar waɗanda aka kashe;
da hannunka mai ƙarfi ka watsar da abokan gābanka.
11 Sammai naka ne, haka kuma duniya;
ka kafa duniya da dukan abin da yake cikinta.
12 Ka halicce arewa da kudu;
Tabor da Hermon suna rera don farin ciki ga sunanka.
13 Hannunka mai iko ne;
hannunka yana da ƙarfi, hannunka na dama ya sami ɗaukaka.
14 Adalci da gaskiya su ne tushen kursiyinka;
ƙauna da aminci suna tafiya a gabanka.
15 Masu albarka ne waɗanda suka koyi yin maka kirari
waɗanda suke tafiya cikin hasken da yake gabanka, Ubangiji.
16 Suna farin ciki a cikin sunanka dukan yini;
suna samun ɗaukaka cikin adalcinka.
17 Gama kai ne ɗaukakarsu da ƙarfinsu,
kuma ta wurin alherinka ka ɗaukaka ƙahonka.†ƙaho a nan na kwatanta mai ƙarfi.
18 Tabbatacce, garkuwarmu ta Ubangiji ce,
ta sarkinmu ce, da kuma ta Mai Tsarki na Isra’ila ce.
19 Ka taɓa yin magana cikin wahayi,
ga mutanenka masu aminci ka ce,
“Na ba wa jarumi ƙarfi;
na ɗaukaka saurayi daga cikin mutane.
20 Na sami Dawuda bawana;
da mai na mai tsarki na shafe shi.
21 Hannuna zai kasance tare da shi;
tabbatacce hannuna zai ƙarfafa shi.
22 Babu abokin gāban da zai sa yă biya haraji;
babu mugun mutumin da zai danne shi.
23 Zan murƙushe maƙiyansa a gabansa
in kashe dukan abokan gābansa.
24 Amintacciya ƙaunata za tă kasance tare da shi,
kuma ta wurin sunana za a ɗaukaka ƙahonsa.
25 Zan sa hannunsa a bisa teku,
hannunsa na dama a bisa koguna.
26 Zai yi kira gare ni yă ce, ‘Kai ne Mahaifina,
Allahna, Dutse mai cetona.’
27 Zan kuma naɗa shi ɗan farina,
mafi ɗaukaka cikin sarakunan duniya.
28 Zan ci gaba da ƙaunarsa har abada,
alkawarina da shi ba zai taɓa fasa ba.
29 Zan kafa zuriyarsa har abada,
kursiyinsa muddin sammai suna nan.
30 “In ’ya’yansa maza suka yashe dokata
ba su kuwa bi ƙa’idodina ba,
31 in suka take ƙa’idodina
suka kuma kāsa kiyaye umarnaina,
32 zan hukunta zunubinsu da sanda,
laifinsu da bulala;
33 amma ba zan ɗauke ƙaunata daga gare shi ba,
ba kuwa zan taɓa rasa cika amincina ba.
34 Ba zan take alkawarina ba
ko in canja abin da leɓunana suka ambata.
35 Sau ɗaya ba ƙari, na rantse da tsarkina,
ba kuwa zan yi ƙarya wa Dawuda ba,
36 cewa zuriyarsa za tă ci gaba har abada
kuma kursiyinsa zai dawwama a gabana kamar rana;
37 zai kahu har abada kamar wata,
amintacciyar shaida a cikin sarari.”
Sela
38 Amma ka ƙi, ka yi ƙyama
ka kuma yi fushi sosai da shafaffenka.
39 Ka soke alkawarin da ka yi da bawanka
ka kuma ƙazantar da rawaninsa a ƙura.
40 Ka rurrushe dukan katangansa
ka sa kagaransa suka zama kufai.
41 Dukan waɗanda suka wuce sun washe shi;
ya zama abin dariya wajen maƙwabtansa.
42 Ka ɗaukaka hannun dama na maƙiyansa;
ka sa dukan abokan gābansa suna farin ciki.
43 Ka juye bakin takobinsa
ba ka kuma taimake shi a cikin yaƙi ba.
44 Ka kawo ƙarshen darajarsa
ka kuma jefar da kursiyinsa ƙasa.
45 Ka rage kwanakin ƙuruciyarsa;
ka rufe shi da mayafin kunya.
Sela
46 Har yaushe, ya Ubangiji za ka ɓoye? Za ka ɓoye har abada ne?
Har yaushe fushinka zai yi ta ci kamar wuta?
47 Ka tuna yadda raina mai wucewa ne.
Gama ka halicce dukan mutane ba amfani!
48 Wanda mutum ne zai rayu da ba zai ga mutuwa ba,
ko yă cece kansa daga ikon kabari?
Sela
49 Ya Ubangiji, ina ƙaunar mai girma ta dā,
wadda cikin amincinka ka rantse wa Dawuda?
50 Ka tuna, Ubangiji, yadda aka yi wa bawanka ba’a,
yadda na jimre a zuciyata da zage-zagen dukan al’ummai,
51 zage-zagen da abokan gābanka suka yi mini, ya Ubangiji,
da suka yi wa kowane matakin da shafaffenka ya ɗauka.
52 Yabo ya tabbata ga Ubangiji har abada!
Amin kuma Amin.
<- Zabura 88Zabura 90 ->
*^ Kan magana, mai yiwuwa kalmar waƙa ce.
†Zabura 89:17 ƙaho a nan na kwatanta mai ƙarfi.