Link to home pageLanguagesLink to all Bible versions on this site
Zabura 82
Zabura ta Asaf.
1 Allah yana shugabanta cikin babban taro;
yakan zartar da hukunci a cikin “alloli”.
 
2 “Har yaushe za ku kāre marasa adalci
ku kuma goyi bayan mugaye?
Sela
3 Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu;
ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya.
4 Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata;
ku kuɓutar da su daga hannun mugaye.
 
5 “Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba.
Suna yawo cikin duhu;
an girgiza dukan tussan duniya.
 
6 “Na ce, ‘Ku “alloli” ne;
dukanku ’ya’yan Mafi Ɗaukaka’ ne.
7 Amma za ku mutu kamar mutum kurum;
za ku fāɗi kamar duk wani mai mulki.”
 
8 Ka tashi, ya Allah, ka shari’anta duniya,
gama dukan al’ummai gādonka ne.

<- Zabura 81Zabura 83 ->