Zabura 80
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Mai muryar “Lilin Alkawari.” Na Asaf. Zabura ce.
1 Ka ji mu, ya Makiyayin Isra’ila,
kai da ka bishe Yusuf kamar garke.
Kai da kake zaune a kursiyi tsakanin kerubobi,
ka haskaka 2 a gaban Efraim, Benyamin da Manasse.
Ka tā da ƙarfinka;
ka zo ka cece mu.
3 Ka mai da mu, ya Allah;
ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu,
za mu kuwa cetu.
4 Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki,
har yaushe fushinka zai yi ta ƙuna
a kan addu’o’in mutanenka?
5 Ka ciyar da su da burodin hawaye;
ka sa suka sha hawaye ta cikakken kwaf.
6 Ka mai da mu abin faɗa ga maƙwabtanmu,
kuma abokan gābanmu suna mana ba’a.
7 Ka mai da mu, ya Allah Maɗaukaki;
ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu
za mu kuwa cetu.
8 Ka fitar da inabi daga Masar;
ka kori al’ummai ka kuma dasa shi.
9 Ka gyara wuri saboda shi,
ya kuwa yi saiwa ya cike ƙasa.
10 Aka rufe duwatsu da inuwarsa,
manya-manyan itatuwan al’ul da rassansa.
11 Ya miƙe rassansa zuwa Teku
tohonsa har zuwa Kogi.
12 Me ya sa ka rurrushe bangayensa
don duk masu wucewa su tsinke ’ya’yan inabinsa?
13 Aladu daga kurmi suna ɓarnatar da shi
halittun gonaki kuma suna cinsa.
14 Ka komo wurinmu, ya Allah Maɗaukaki!
Ka duba daga sama ka gani!
Ka lura da wannan inabi,
15 saiwar da hannun damarka ya dasa,
ɗan da ka renar wa kanka.
16 An yanke inabinka, an ƙone shi da wuta;
a tsawatawarka mutanenka sun hallaka.
17 Bari hannunka yă zauna a kan mutumin da yake hannun damarka,
ɗan mutum da ka renar wa kanka.
18 Ta haka ba za mu juye mu bar ka ba;
ka rayar da mu, za mu kuwa kira bisa sunanka.
19 Ka mai da mu, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki;
ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu,