Zabura 40
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce.
1 Na jira da haƙuri ga Ubangiji;
ya juya wurina ya kuma ji kukata.
2 Ya ɗaga ni daga rami marar fāɗi,
daga laka da taɓo;
ya sa ƙafafuna a kan dutse
ya kuma ba ni tsayayyen wuri don in tsaya.
3 Ya sa sabuwar waƙa a bakina,
waƙar yabo ga Allahna.
Da yawa za su gani su tsorata
su kuma dogara ga Ubangiji.
4 Mai albarka ne mutumin
da ya mai da Ubangiji abin dogararsa,
wanda ba ya kula da masu girman kai,
waɗanda suka juya ga allolin ƙarya.
5 Da yawa ne, ya Ubangiji Allahna,
abubuwan banmamakin da ka aikata.
Abubuwan da ka shirya mana.
Ba wanda zai iya faɗa maka su;
a ce zan yi magana in faɗe su,
za su wuce gaban misali a furta.
6 Hadaya da sadaka ba ka sha’awa,
amma kunnuwana ka huda;
hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka bukata.
7 Sa’an nan na ce, “Ga ni, na zo,
kamar yadda yake a rubuce game da ni cikin littafi.
8 Ina sha’awar aikata nufinka, ya Allahna;
dokar tana cikin zuciyata.”
9 Na yi shelar adalcinka cikin babban taro;
ba na rufe leɓunana,
kamar yadda ka sani, ya Ubangiji.
10 Ba na ɓoye adalcinka cikin zuciyata;
ina maganar amincinka da cetonka.
Ban ɓoye ƙaunarka da gaskiyarka
a gaban taron jama’arka mai girma ba.
11 Kada ka hana mini jinƙanka, ya Ubangiji;
bari ƙaunarka da gaskiyarka kullum su kāre ni.
12 Gama damuwoyin da suka wuce misali sun kewaye ni;
zunubaina sun mamaye ni, kuma ba na iya gani.
Sun fi gashin kaina yawa,
har ma na fid da zuciya.
13 Ka ji daɗin cetona, ya Ubangiji;
Ya Ubangiji, ka zo da sauri ka taimake ni.
14 Bari masu neman raina
su sha kunya su kuma rikice;
bari dukan waɗanda suke neman lalacewata
su koma baya da kunya.
15 Bari masu ce mini, “Allah yă ƙara!”
Su sha mamaki saboda kunyar da za su sha.
16 Amma bari dukan masu nemanka
su yi farin ciki su kuma yi murna a cikinka;
bari waɗanda suke ƙaunar cetonka kullum su ce,
“Ubangiji mai girma ne!”
17 Ni dai matalauci ne da mai bukata;
bari Ubangiji yă tuna da ni.
Kai ne taimakona da mai cetona;