Link to home pageLanguagesLink to all Bible versions on this site
Zabura 35
Ta Dawuda.
1 Yi hamayya, ya Ubangiji, da waɗanda suke hamayya da ni;
yi faɗa da waɗanda suke faɗa da ni.
2 Ka ɗauki garkuwa da kuma makami;
ka tashi ka taimake ni.
3 Ka ɗaga māshi da kuma abin da ake jefa*Ko kuwa ka kuwa tare hanya
a kan waɗanda suke fafarata.
Ka ce wa raina,
“Ni ne cetonka.”
 
4 Bari waɗanda suke neman raina
su sha kunya a kuma kunyatar da su;
bari waɗanda suke shirya lalacewata
su juya da baya su ruɗe.
5 Bari su zama kamar yayi a gaban iska,
mala’ikan Ubangiji kuma yana korarsu;
6 bari hanyarsu tă yi duhu ta kuma yi santsi,
mala’ikan Ubangiji kuma yana fafararsu.
 
7 Da yake sun ɓoye tarko domina ba dalili
kuma babu dalili suka haƙa mini rami,
8 bari lalaci yă kama su ba zato,
bari tarkon da suka ɓoye yă kama su,
bari su fāɗa cikin ramin, yă kai ga lalacinsu.
9 Sa’an nan raina zai cika da farin ciki a cikin Ubangiji
in yi kuma murna a cikin cetonsa.
10 Dukan raina zai ce,
“Wane ne kamar ka, ya Ubangiji?
Ka kuɓutar da matalauta daga waɗanda suka fi ƙarfinsu,
matalauta da masu bukata daga waɗanda suke musu fashi.”
 
11 Shaidu marasa imani sun fito;
suna mini tambaya a kan abubuwan da ban san kome a kai ba.
12 Suna sāka alherin da na yi musu da mugunta
suka bar raina da nadama.
13 Duk da haka sa’ad da suke ciwo, na sanya rigar makoki
na ƙasƙantar da kaina da azumi.
Sa’ad da aka mayar mini da addu’o’i babu amsa,
14 nakan yi ta yawo ina makoki
sai ka ce yadda nake yi wa abokina ko ɗan’uwana.
Nakan sunkuyar da kaina cikin baƙin ciki
sai ka ce ina kuka domin mahaifiyata.
15 Amma sa’ad da na yi tuntuɓe, sukan taru suna murna;
masu kai hari sun taru a kaina sa’ad da ban sani ba.
Suna ɓata mini suna ba tsagaitawa.
16 Kamar marasa sani Allah suna mini riyar ba’a;
Suna hararata da ƙiyayya.
 
17 Ya Ubangiji, har yaushe za ka ci gaba da zuba ido kawai?
Ka kuɓutar da raina daga farmakinsu,
raina mai daraja daga waɗannan zakoki.
18 Zan yi godiya cikin taro mai girma;
cikin ɗumbun mutane zan yabe ka.
19 Kada ka bar maƙaryatan nan,
su yi farin ciki a kaina;
kada ka bar waɗanda suke ƙina ba dalili,
su ji daɗin baƙin cikina.
20 Ba sa maganar salama
sukan ƙirƙiro zage-zagen ƙarya
a kan waɗanda suka zama shiru a ƙasar.
21 Sukan wage mini bakinsu suna cewa, “Allah yă ƙara!
Da idanunmu mun gani.”
 
22 Ya Ubangiji, ka ga wannan; kada ka yi shiru.
Kada ka yi nisa da ni, ya Ubangiji.
23 Ka farka, ka kuma tashi ka kāre ni!
Ka yi mini faɗa, ya Allahna da shugabana.
24 Ka nuna ni marar laifi ne ciki adalcinka,
Ya Ubangiji Allahna; kada ka bari su yi farin ciki a kaina.
25 Kada ka bari su ce wa kansu, “Allah yă ƙara, dā ma abin da mun so ke nan!”
Ko su ce, “Mun haɗiye shi.”
 
26 Bari dukan waɗanda suke farin ciki a kaina a wahalata
su sha kunya su kuma ruɗe;
bari dukan waɗanda suke ɗaukar kansu sun fi ni
su sha kunya da wulaƙanci.
27 Bari waɗanda suke murna saboda nasarata
su yi sowa don farin ciki da murna;
bari kullum su riƙa cewa, “A ɗaukaka Ubangiji,
wanda yake farin ciki da zaman lafiyar bawansa.”
 
28 Harshena zai yi zancen adalcinka
da kuma yabonka dukan yini.

<- Zabura 34Zabura 36 ->