Zabura 33
1 Ku rera da farin ciki ga Ubangiji ku adalai;
daidai ne masu gaskiya su yabe shi.
2 Ku yabi Ubangiji da garaya;
ku yi kiɗi gare shi da molo mai tsirkiya goma.
3 Ku rera masa sabuwar waƙa;
ku yi kiɗi da gwaninta, ku kuma yi sowa don farin ciki.
4 Gama maganar Ubangiji daidai ne da kuma gaskiya;
yana da aminci cikin kome da yake yi.
5 Ubangiji yana ƙaunar adalci
duniya ta cika da ƙaunarsa marar ƙarewa.
6 Ta wurin maganar Ubangiji aka yi sammai,
rundunar taurarinsu kuwa da numfashin bakinsa.
7 Ya tattara ruwan teku cikin tuluna;*Ko kuwa teku sai ka ce a tsibi
ya sa zurfafa cikin gidajen ajiya.
8 Bari dukan duniya ta ji tsoron Ubangiji;
bari dukan mutanen duniya su girmama shi.
9 Gama ya yi magana, abu ya kuwa kasance;
ya umarta, ya kuwa tsaya daram.
10 Ubangiji yakan soke shirye-shiryen al’ummai;
yakan wofintar da manufofin mutane.
11 Amma shirye-shiryen Ubangiji kan tsaya daram har abada,
manufofin zuciyarsa kuwa har dukan zamanai.
12 Mai farin ciki ce al’ummar da Allah ne Ubangijinta,
mutanen da ya zaɓa don gādonsa.
13 Daga sama Ubangiji ya duba
ya kuwa ga dukan ’yan adam;
14 daga mazauninsa yana lura
da dukan waɗanda suke zama a duniya,
15 shi da ya yi zukatan duka,
wanda yake kula da kome da suke yi.
16 Babu sarkin da ake ceto ta wurin yawan mayaƙansa;
ba jarumin da kan kuɓuta ta wurin yawan ƙarfinsa.
17 Dogara a kan doki don ceto banza ne;
duk da yawan ƙarfinsa ba ya ceto.
18 Amma idanun Ubangiji suna a kan wanda yake tsoronsa,
a kan waɗanda suke sa zuciya cikin ƙaunarsa marar ƙarewa,
19 don yă cece su daga mutuwa
ya bar su da rai a lokacin yunwa.
20 Muna jiran Ubangiji da bege;
shi ne taimakonmu da garkuwarmu.
21 A cikinsa zukatanmu na farin ciki,
gama mun dogara cikin sunansa mai tsarki.
22 Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zauna a kanmu, ya Ubangiji,
ko ma da muke sa begenmu a gare ka.
<- Zabura 32Zabura 34 ->
*Zabura 33:7 Ko kuwa teku sai ka ce a tsibi