Zabura 15
Zabura ta Dawuda.
1 Ubangiji, wa zai zauna cikin wuri mai tsarkinka?
Wa zai zauna a kan tudunka mai tsarki?
2 Sai wanda ba shi da laifi
kuma yana yin abin da yake daidai,
wanda yake faɗin gaskiya daga zuciyarsa
3 ba ya kuwa ɓata sunan wani da harshensa,
wanda ba ya yi wa maƙwabcinsa mugunta
ba ya kuwa baza jita-jita a kan ɗan’uwansa,
4 wanda yake ƙin mugun mutum
amma yakan girmama masu tsoron Ubangiji,
yakan cika alkawarinsa
ko da ma ya zafe shi,
5 wanda yake ba da rance ba tare da ruwa ba
kuma ba ya karɓan cin hanci don yă kā da marar laifi.
Shi wanda yake yin waɗannan abubuwa