Link to home pageLanguagesLink to all Bible versions on this site
Zabura 131
Waƙar haurawa. Ta Dawuda.
1 Zuciyata ba mai girman kai ba ce, ya Ubangiji,
idanuna ba sa fariya;
ban dami kaina da manyan al’amura ba
ko abubuwan da suka sha ƙarfina.
2 Amma na haƙura na kuma kwantar da raina;
kamar yaron da aka yaye tare da mahaifiyarsa,
kamar yaron da aka yaye haka raina yake a cikina.
 
3 Ya Isra’ila, sa zuciyarka ga Ubangiji
yanzu da har abada kuma.

<- Zabura 130Zabura 132 ->