Zabura 130
Waƙar haurawa.
1 Daga cikin zurfafa na yi kuka gare ka, ya Ubangiji;
2 Ya Ubangiji, ka ji muryata.
Bari kunnuwanka su saurara
ga kukata ta neman jinƙai.
3 In kai, ya Ubangiji, za ka lissafta zunubai,
Ya Ubangiji, wa zai tsaya?
4 Amma tare da kai akwai gafartawa,
saboda haka ake tsoronka.
5 Zan jira Ubangiji, raina zai jira,
kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata.
6 Raina na jiran Ubangiji
fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya,
fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya.
7 Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji,
gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa
kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa.
8 Shi kansa zai fanshi Isra’ila