Link to home pageLanguagesLink to all Bible versions on this site
Zabura 124
Waƙar haurawa. Ta Dawuda.
1 Da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba,
bari Isra’ila yă ce,
2 da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba
sa’ad da aka auka mana,
3 sa’ad da fushinsu ya ƙuna a kanmu,
ai, da sun haɗiye mu da rai;
4 da rigyawa ta kwashe mu,
da ambaliya ta rufe mu.
5 Da ruwa mai hauka
ya share mu ƙaf.
 
6 Yabo ya tabbata ga Ubangiji,
wanda bai bari aka yayyage mu da haƙoransu ba.
7 Mun tsira kamar tsuntsu
daga tarkon mai farauta;
an tsinke tarko,
muka kuwa tsira.
8 Taimakonmu yana a sunan Ubangiji,
Wanda ya yi sama da ƙasa.

<- Zabura 123Zabura 125 ->