Zabura 122
Waƙar haurawa. Ta Dawuda.
1 Na yi farin ciki tare da waɗanda suka ce da ni,
“Bari mu tafi gidan Ubangiji.”
2 Ƙafafunmu suna tsaye
a ƙofofinki, ya Urushalima.
3 An gina Urushalima kamar birnin
da aka yi a harhaɗe wuri guda.
4 A can ne kabilu suke haurawa,
kabilan Ubangiji,
don su yabi sunan Ubangiji
bisa ga farillan da aka ba wa Isra’ila.
5 A can kursiyoyin shari’a yake tsaye,
kursiyoyin gidan Dawuda.
6 Ku yi addu’a don salamar Urushalima,
“Bari waɗanda suke ƙaunarki su zauna lafiya.
7 Bari salama ta kasance a katangarki
zaman lafiya kuma a fadodinki.”
8 Saboda ’yan’uwana da kuma abokaina,
zan ce, “Salama tă kasance tare da ke.”
9 Saboda gidan Ubangiji Allahnmu,