Link to home pageLanguagesLink to all Bible versions on this site
Zabura 121
Waƙar haurawa.
1 Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai,
ta ina ne taimakona zai zo?
2 Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji,
wanda ya kafa sama da ƙasa.
 
3 Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba,
shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba;
4 tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila
ba ya gyangyaɗi ko barci.
 
5 Ubangiji yana tsaronka,
Ubangiji ne inuwa a hannun damanka;
6 rana ba za tă buge ka cikin yini ba
balle wata da dare.
 
7 Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa,
zai tsare ranka;
8 Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka
yanzu da har abada kuma.

<- Zabura 120Zabura 122 ->