Zabura 113
1 Yabi Ubangiji.*Da Ibraniyanci Hallelu Ya, haka ma a aya 9.
Ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji,
ku yabi sunan Ubangiji.
2 Bari a yabi sunan Ubangiji,
yanzu da har abada kuma.
3 Daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa,
a yabi sunan Ubangiji.
4 Ana ɗaukaka Ubangiji a bisa dukan al’ummai,
ɗaukakarsa a bisa sammai
5 Wane ne yake kamar Ubangiji Allahnmu,
Wannan mai zama a kursiyi can bisa,
6 wanda yake sunkuya yă dubi
sammai da duniya?
7 Yakan tā da matalauta daga ƙura
yakan ɗaga mabukata daga tarin toka;
8 ya zaunar da su tare da sarakuna,
tare da sarakunan mutanensu.
9 Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidanta
ta zama kamar mahaifiyar ’ya’ya mai farin ciki.