Link to home pageLanguagesLink to all Bible versions on this site
LITTAFI NA BIYAR
107
Zabura 107–150
1 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi;
ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
 
2 Bari fansassu na Ubangiji su faɗa wannan,
su da aka fansa daga hannun maƙiyi,
3 su da ya tattara daga ƙasashe,
daga gabas da yamma, daga arewa da kudu.
 
4 Waɗansu sun yi ta yawo a jejin hamada,
ba su sami hanya zuwa birnin da za su zauna ba.
5 Sun ji yunwa da ƙishirwa,
suka kuma fid da zuciya.
6 Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu,
ya kuma cece su daga damuwarsu.
7 Ya bishe su ta miƙaƙƙiyar hanya
zuwa birnin da za su zauna.
8 Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa
da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane,
9 gama yana shayar da masu ƙishirwa
yana kuma ƙosar da mayunwata da abubuwa masu kyau.
 
10 Waɗansu sun zauna a cikin duhu da kuma zurfin ɓacin rai,
’yan kurkuku suna wahala cikin sarƙoƙin ƙarfe,
11 gama sun yi tayarwa a kan maganar Allah
suka ƙi shawarar Mafi Ɗaukaka.
12 Saboda haka ya ba da su ga aiki mai wuya;
suka yi tuntuɓe, kuma ba mai taimako.
13 Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu,
ya kuwa cece su daga damuwarsu.
14 Ya fitar da su daga duhu da zurfin ɓaci rai
ya tsintsinke sarƙoƙinsu.
15 Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa
da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane,
16 gama ya farfashe ƙofofin tagulla
ya kuma ragargaza ƙyamaren ƙarfe.
 
17 Waɗansu suka zama wawaye ta wurin hanyoyinsu na tayarwa
suka kuwa sha wahala saboda laifofinsu.
18 Ba su so su ga abinci ba
suka kuwa kai bakin mutuwa.
19 Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu,
ya kuwa cece su daga damuwarsu.
20 Ya ba da umarninsa ya kuma warkar da su
ya kuɓutar da su daga kabari.
21 Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa
da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane.
22 Bari su miƙa hadaya ta godiya
su kuma ba da labarin ayyukansa da waƙoƙin farin ciki.
 
23 Waɗansu suka yi tafiya a teku cikin jiragen ruwa;
su ’yan kasuwa ne a manyan ruwaye.
24 Sun ga ayyukan Ubangiji,
ayyukansa masu banmamaki a cikin zurfin teku.
25 Gama ya yi magana ya kuma sa iska mai ƙarfi ta tashi
ya ɗaga raƙuman ruwa sama.
26 Suka hau zuwa sammai suka kuma tsinduma cikin zurfafa;
a cikin azabarsu sai ƙarfin halinsu ya karai.
27 Suka yi tangaɗi suna tuntuɓe kamar bugaggu;
suka kuma kai ga ƙarshen dabararsu.
28 Sai suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu,
ya kuwa fitar da su daga damuwarsu.
29 Ya kwantar da hadiri suka yi tsit;
raƙuman ruwan teku suka yi shiru.
30 Suka yi murna sa’ad da wuri ya kwanta,
ya kuma bishe su zuwa inda suka so su kai.
31 Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa
da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane.
32 Bari su ɗaukaka shi cikin taron mutane
su kuma yabe shi cikin taron dattawa.
 
33 Ya mai da koguna suka zama hamada,
maɓulɓulai masu gudu suka zama ƙasa mai ƙishirwa,
34 ƙasa mai amfani kuma suka zama gishiri marar amfani,
saboda muguntar waɗanda suka zauna a can.
35 Ya mai da hamada ya zama tafkunan ruwa
busasshiyar ƙasa kuma zuwa maɓulɓulai masu gudu;
36 a can ya kai mayunwata su yi zama,
ya kuma samo birnin da za su zauna.
37 Suka yi shuka a gonaki suka dasa inabi
suka kuma girbe amfani gona;
38 ya albarkace su, yawansu kuma ya ƙaru,
bai kuwa bar garkunansu suka ragu ba.
 
39 Sa’an nan yawansu ya ragu, aka kuma ƙasƙantar da su
ta wurin danniya, bala’i da kuma baƙin ciki;
40 shi da yake kawo reni a kan manyan mutane
ya sa suka yi ta yawo a cikin jejin da ba hanya.
41 Amma ya fid da mabukata daga wahalarsu
ya kuma ƙara iyalansu da tumakinsu.
42 Masu yin gaskiya suka gani suka yi farin ciki
amma dukan mugaye suka rufe bakunansu.
 
43 Duk mai hikima, bari yă ji waɗannan abubuwa
yă kuma lura da ƙauna mai girma ta Ubangiji.

<- Zabura 106Zabura 108 ->