Link to home pageLanguagesLink to all Bible versions on this site
11
1 Ubangiji yana ƙyamar ma’aunan zamba,
amma ma’aunin da suke daidai ne abin farin cikinsa.
 
2 Sa’ad da girman kai ya zo, sai shan kunya ta zo,
amma hikima kan zo tare da ƙasƙantar da kai.
 
3 Mutuncin masu aikata gaskiya takan bi da su,
amma marasa aminci sukan hallaka ta wurin cin amanar da suke yi.
 
4 Dukiya ba ta da amfani a ranar fushi,
amma adalci kan yi ceto daga mutuwa.
 
5 Adalcin marasa laifi kan miƙe hanyarsu,
amma akan ƙasƙantar da mugaye ta wurin muguntarsu.
 
6 Adalcin masu aikata gaskiya kan cece su,
amma rashin aminci tarko ne ga mugayen sha’awace-sha’awace.
 
7 Sa’ad da mugu ya mutu, sa zuciyarsa kan hallaka;
dukan abin da ya sa zuciya daga ikonsa ba ya amfana kome.
 
8 Akan kuɓutar da mai adalci daga wahala,
sai ta dawo wa mugu a maimako.
 
9 Da bakinsa marar sanin Allah kan hallaka maƙwabcinsa,
amma ta wurin sani mai adalci kan kuɓuta.
 
10 Sa’ad da adali ya yi nasara, birnin kan yi farin ciki;
sa’ad da mugu ya hallaka, akwai sowa ta farin ciki.
 
11 Ta wurin albarkar mai aikata gaskiya birni kan ƙasaita,
amma ta wurin bakin mugu akan hallaka birnin.
 
12 Mutum da ba shi da azanci kan ki maƙwabci,
amma mutum mai fahimi kan ƙame harshensa.
 
13 Gulma yakan lalace yarda,
amma mutum mai aminci kan kiyaye asiri.
 
14 Saboda rashin jagora al’umma takan fāɗi,
amma masu ba da shawara da yawa kan tabbatar da nasara.
 
15 Duk wanda ya ɗauki lamunin wani tabbatacce zai sha wahala,
amma duk wanda ya ƙi ya sa hannu a ɗaukar lamuni ba ruwansa.
 
16 Mace mai hankali na samu bangirma,
amma azzalumai za su sami dukiya.
 
17 Mutumin kirki kan ribance kansa,
amma mugu kan kawo wa kansa wahala.
 
18 Mugun mutum kan sami albashin ƙarya
amma shi da ya shuka adalci zai girbe lada tabbatacce.
 
19 Mutum mai adalci da gaske yakan sami rai,
amma shi da ya duƙufa ga aikata mugunta kan tarar da mutuwarsa.
 
20 Ubangiji yana ƙyamar mutane masu muguwar zuciya
amma yana jin daɗin waɗanda hanyoyinsu ba su da laifi.
 
21 Ka tabbata da wannan. Mugaye ba za su tafi babu hukunci ba,
amma waɗanda suke masu adalci za su tafi babu hukunci.
 
22 Kamar zinariya a hancin alade
haka kyan mace wadda ba ta da hankali.
 
23 Sha’awar adalai kan ƙare kawai a aikata alheri,
amma sa zuciyar mugaye kan ƙarasa kawai a fushi.
 
24 Wani mutum kan bayar hannu sake, duk da haka yakan sami fiye;
wani yakan riƙe abin da ba nasa ba, amma sai ya ƙarasa cikin talauci.
 
25 Mutum mai kyauta zai azurta;
shi da yakan taimake waɗansu, za a taimake shi.
 
26 Mutane kan la’anci mai ɓoye hatsi yana jira ya yi tsada,
amma albarka kan zauna a kan wanda yake niyya ya sayar.
 
27 Duk mai nema alheri kan sami alheri,
amma mugu kan zo wa wanda yake nemansa.
 
28 Duk wanda ya dogara ga arzikinsa zai fāɗi,
amma adali zai yi nasara kamar koren ganye.
 
29 Duk wanda ya kawo wahala wa iyalinsa zai gāji iska kawai,
kuma wawa zai zama bawan masu hikima.
 
30 ’Ya’yan itacen adali itacen rai ne,
kuma duk mai samun rayuka mai hikima ne.
 
31 In masu adalci sun sami abin da ya dace da su a duniya,
yaya zai zama ga marasa sanin Allah da kuma masu zunubi!