1 Saboda haka ’yan’uwana, ku da nake ƙauna, nake kuma marmarin ganinku, ku da kuke farin cikina da kuma rawanina, ku dāge ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna!
2 Ina roƙon Yuwodiya ina kuma roƙon Sintike, su yi zaman lafiya da juna saboda su na Ubangiji ne. 3 I, ina kuma roƙonka, abokin famata, ka taimaki matan nan waɗanda suka yi fama aikin bishara tare da ni, haka ma Kilemen da kuma sauran abokan aikina, waɗanda sunayensu suna cikin littafin rai.
8 A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan. 9 Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.
14 Duk da haka kun kyauta da kuka yi tarayya da ni cikin wahalolina. 15 Ban da haka, kamar yadda ku Filibbiyawa kuka sani, a farkon kwanakin da kuka ji bishara, sa’ad da na tashi daga Makidoniya, babu wata ikkilisiyar da tă yi tarayya da ni a fannin bayarwa da karɓa, sai ku kaɗai; 16 gama ko sa’ad da nake a Tessalonika ma, kun aiko mini da taimako sau da sau sa’ad da nake cikin bukata. 17 Ba cewa ina neman kyauta ba ne, sai dai ina neman abin da za a ƙara a kan ribarku. 18 An biya ni duka, biyan da ya wuce misali. Bukatata ta biya, da yake na karɓi kyautarku da kuka aiko ta hannun Afaforiditus. Baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai. 19 Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.
20 Ɗaukaka ta tabbata ga Allahnmu da Ubanmu har abada abadin. Amin.
22 Dukan tsarkaka suna gaishe ku, musamman waɗanda suke na gidan Kaisar.
- a Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā ba su da Amin.