1 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “Ka umarci Isra’ilawa cewa, ‘Ku tabbatar kun miƙa mini hadaya ta abinci ta wuta mai daɗin ƙanshi a gare ni, a daidai lokaci.’ 3 Ka gaya musu, ‘Ga hadaya ta ƙonawa ta kowace rana, da za ku miƙa wa Ubangiji, raguna biyu, bana ɗaya-ɗaya, marasa lahani. 4 A miƙa rago ɗaya da safe, ɗaya kuma da yamma, 5 tare da hadaya ta lallausan gari kashi ɗaya bisa goma na efan, kwaɓaɓɓe da kwalaba ɗaya na man zaitun mafi kyau. 6 Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kullum wadda aka kafa a Dutsen Sinai, don daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. 7 Hadaya ta sha, za tă zama kwalaba ɗaya na ruwan inabi, da ɗan rago guda. Za a kwarara hadaya ta sha ga Ubangiji a wuri mai tsarki. 8 Ɗayan ɗan ragon kuma za a miƙa shi da yamma, tare irin hadaya ta lallausan gari, da hadaya ta sha da ka yi da safe. Wannan hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
16 “ ‘Za a yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji a rana ta goma sha huɗu ga wata na fari. 17 A rana ta goma sha biyar ga wannan wata, za a yi biki; kwana bakwai za a ci burodi marar yisti. 18 A rana ta farko, za ku yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi na kullum ba. 19 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimai biyu, rago ɗaya, da ’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya; dukansu kuma marasa lahani ga Ubangiji. 20 Da kowane bijimi, a shirya kashi ɗaya bisa uku na efan lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai; da rago guda kuwa, a shirya kashi biyu bisa goma na efan lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai; 21 da kowane ’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma. 22 A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara. 23 Ku shirya wannan tare da hadaya ta ƙonawa ta kowace safiya. 24 Ta haka za a shirya abinci don hadayar da aka yi da wuta, kowace rana, har kwana bakwai don daɗin ƙanshi ga Ubangiji; a shirya shi haɗe da hadaya ta ƙonawa ta kullum, da kuma hadaya ta sha. 25 A rana ta bakwai, za ku yi tsattsarkan taro, amma ba za a yi aikin da aka saba yi kullum ba.
26 “ ‘A ranar nunan fari, sa’ad da za ku miƙa wa Ubangiji hadayar sabon hatsi, a lokacin Bikin Makoni, za a yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi ba. 27 A miƙa hadaya ta ƙonawa da ’yan bijimai biyu, rago ɗaya da ’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 28 Da kowane bijimi a kasance da hadaya ta lallausan gari kashi uku bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai; da rago kuwa, a kasance da hadaya ta lallausan gari kashi biyu bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai; 29 da kowane ’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma. 30 A haɗa da bunsuru guda don yin muku kafara. 31 A miƙa waɗannan tare da hadayarsu ta sha, haɗe da hadaya ta ƙonawa ta kullum, da kuma hadayarta ta sha. A tabbata dabbobin nan marasa lahani ne.
<- Ƙidaya 27Ƙidaya 29 ->