1 Bala’am ya ce, “Ka gina mini bagadai bakwai a nan, ka shirya mini bijimai bakwai da raguna bakwai.” 2 Balak ya yi yadda Bala’am ya faɗa, sai su biyu suka miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.
3 Sa’an nan Bala’am ya ce wa Balak, “Tsaya nan kusa da hadayarka, ni kuwa in koma wani wurin da yake a kaɗaice. Wataƙila Ubangiji zai sadu da ni. Duk abin da ya bayyana mini, zan faɗa maka.” Sai ya haura kan wani wurin da yake a kaɗaice a tudun.
4 Allah kuwa ya sadu da Bala’am. Bala’am ya ce, “Na shirya bagadai bakwai, na kuma miƙa bijimi guda da rago guda, a kan kowane bagade.”
5Ubangiji ya ba wa Bala’am saƙo ya ce, “Ka koma wurin Balak, ka faɗa masa wannan saƙo.”
6 Saboda haka, sai Bala’am ya koma wurin Balak ya same shi tsaye a kusa da hadayarsa, tare da dukan dattawan Mowab. 7 Sai Bala’am ya furta abin da Allah ya faɗa masa ya ce,
“Balak ya kawo ni daga Aram,
sarkin Mowab ya kawo ni daga gabashin duwatsu.
Ya ce, ‘Zo, ka la’anta mini Yaƙub;
zo, ka tsine Isra’ila.’
8 Yaya zan iya la’anta
waɗanda Allah bai la’anta ba?
Yaya zan tsine
waɗanda Ubangiji bai tsine ba?
9 Daga kan duwatsu na gan su,
daga bisa kan tuddai na hange su.
Na ga mutane da suke zaune su kaɗai
ba sa ɗauki kansu ɗaya da al’ummai ba.
10 Wa zai iya ƙidaya ƙurar Yaƙub
ko yă ƙidaya kashi ɗaya bisa huɗu na Isra’ila?
Bari in mutu, mutuwar adali
ƙarshena kuma yă zama kamar nasu!”
11 Balak ya ce wa Bala’am, “Me ke nan ka yi mini? Na kawo ka, ka la’anta abokan gābana, sai ga shi albarka kake sa musu!”
12 Bala’am ya ce, “Ba dole in faɗa abin da Ubangiji ya sa a bakina ba?”
Maganar Bala’am ta biyu na abin da Ubangiji ya faɗa
13 Sa’an nan Balak ya ce masa, “Zo, mu tafi wani wuri inda za ka gan su; a nan kana ganin sashe ne kawai, ba dukansu ba. Daga can kuwa, ka la’anta mini su.” 14 Saboda haka ya ɗauke shi zuwa filin Zofim a ƙwanƙolin Fisga, a can ya gina bagadai bakwai, ya kuma miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.
15 Bala’am ya ce wa Balak, “Tsaya nan kusa da hadayarka, ni kuwa in je in sadu da Ubangiji a can.”
16Ubangiji ya sadu da Bala’am, ya kuma ba shi saƙo ya ce, “Koma wurin Balak ka ba shi wannan saƙo.”
17 Saboda haka ya tafi ya same Balak tsaye a kusa da hadayarsa, tare da dattawan Mowab. Balak ya tambaye Bala’am ya ce, “Mene ne Ubangiji ya ce?”
18 Sai Bala’am ya furta saƙon da aka ba shi ya ce,
25 Sai Balak ya ce wa Bala’am, “Kada ka la’anta su, kada kuma ka sa musu albarka!”
26 Bala’am amsa ya ce, “Ban faɗa maka zan yi kaɗai abin da Ubangiji ya ce ba?”
Maganar Bala’am ta uku na abin da Ubangiji ya faɗa
27 Sai Balak ya ce wa Bala’am, “Zo in kai ka wani wuri. Wataƙila zai gamshi Allah, yă bari ka la’anta mini su daga can.” 28 Balak kuwa ya ɗauki Bala’am zuwa ƙwanƙolin Feyor, wanda yake fuskantar hamada.
29 Bala’am ya ce, “Ka gina mini bagadai bakwai a nan, ka kuma shirya mini bijimai bakwai da raguna bakwai.” 30 Balak ya yi yadda Bala’am ya ce, ya kuwa miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.