3 (Musa kuwa mutum ne mai tawali’u ƙwarai, mafi tawali’u fiye da kowane mutum a duniya.)
4 Nan da nan Ubangiji ya ce wa Musa, da Haruna da kuma Miriyam, “Ku fita ku tafi Tentin Sujada, dukanku uku.” Sai dukansu uku suka tafi. 5 Sai Ubangiji ya sauko a cikin ginshiƙin girgije; ya tsaya a bakin ƙofar Tenti, ya kira Haruna da Miriyam. Sa’ad da su biyu suka gusa gaba, 6 sai ya ce, “Ku ji abin da zan faɗa,
9 Sai fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kansu, ya kuma rabu da su.
10 Da girgijen ya tashi daga bisa Tentin, sai ga Miriyam tsaye, kuturwa, fari fat. Haruna kuwa ya juya wajenta ya ga ta kuturce; 11 sai Haruna ya ce wa Musa, “Ranka yă daɗe, ina roƙonka kada ka hukunta mu, gama zunubin da muka yi, mun yi ne cikin wauta. 12 Kada ka sa ta zama kamar haifaffen mataccen jariri daga cikin mahaifiya wanda rabin jikin ruɓaɓɓe ne.”
13 Saboda haka sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Ya Allah, ina roƙonka ka warkar da ita!”
14 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Da a ce mahaifinta ne ya tofa mata miyau a fuskarta, ashe, ba za tă ji kunya har kwana bakwai ba? A fitar da ita bayan sansani kwana bakwai; bayan haka za a iya dawo da ita.” 15 Haka aka fitar da Miriyam bayan sansani kwana bakwai, mutane kuwa ba su ci gaba da tafiya ba sai da aka dawo da ita.
16 Bayan haka sai mutane suka bar Hazerot suka sauka a Hamadan Faran.
<- Ƙidaya 11Ƙidaya 13 ->