Ƙidaya
1
Ƙidayar yawan mutane
1 Ubangiji ya yi magana da Musa a Tentin Sujada a cikin Hamadar Sinai, a rana ta fari na watan biyu a shekara ta biyu, bayan Isra’ilawa suka fito Masar ya ce, 2 “Ka yi ƙidayan dukan al’umman Isra’ilawa bisa ga iyalansu da kabilarsu, ka rubuta kowa da sunansa bi da bi. 3 Da kai da Haruna za ku lissafta dukan mazan Isra’ila bisa ga sashensu, waɗanda suka kai shekaru ashirin ko fiye, da za su iya shiga soja. 4 Mutum ɗaya daga kowace kabila wanda yake shugaban danginsa, zai taimake ku.
5 “Ga sunayen da za su taimake ku.
“Daga kabilar Ruben, Elizur ɗan Shedeyur;
6 daga kabilar Simeyon, Shelumiyel ɗan Zurishaddai;
7 daga kabilar Yahuda, Nashon ɗan Amminadab;
8 daga kabilar Issakar, Netanel ɗan Zuwar;
9 daga kabilar Zebulun, Eliyab ɗan Helon;
10 daga kabilar ’ya’yan Yusuf,
daga Efraim, Elishama ɗan Ammihud;
daga Manasse, Gamaliyel ɗan Fedazur;
11 daga kabilar Benyamin, Abidan ɗan Gideyoni;
12 daga kabilar Dan, Ahiyezer ɗan Ammishaddai;
13 daga kabilar Asher, Fagiyel ɗan Okran;
14 daga kabilar Gad, Eliyasaf ɗan Deyuwel;
15 daga kabilar Naftali, Ahira ɗan Enan.”
16 Waɗannan su ne mutanen da aka naɗa daga cikin jama’a, shugabannin asalin kabilu. Su ne kuma shugabannin dangogin Isra’ila.
17 Sai Musa da Haruna suka ɗauki sunayen mutanen nan da aka ba su, 18 suka kira dukan al’umma wuri ɗaya a rana ta fari ga wata na biyu. Aka kuwa rubuta mutanen bisa ga asalin kabilansu da iyalansu. Aka kuma rubuta sunayen maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekaru ashirin ko fiye, 19 yadda Ubangiji ya umarci Musa. Da haka ya ƙidaya su a Hamadar Sinai.
20 Daga zuriyar Ruben ɗan fari na Isra’ila. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. 21 Jimillar maza daga mutanen Ruben 46,500 ne.
22 Daga zuriyar Simeyon. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. 23 Jimillar maza daga mutanen Simeyon 59,300 ne.
24 Daga zuriyar Gad. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. 25 Jimillar maza daga mutanen Gad 45,650 ne.
26 Daga zuriyar Yahuda. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. 27 Jimillar maza daga mutanen Yahuda 74,600 ne.
28 Daga zuriyar Issakar. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. 29 Jimillar maza daga mutanen Issakar 54,400 ne.
30 Daga zuriyar Zebulun. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. 31 Jimillar maza daga mutanen Zebulun 57,400 ne.
32 Daga ’ya’yan Yusuf.
Daga zuriyar Efraim. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. 33 Jimillar maza daga mutanen Efraim 40,500 ne.
34 Daga zuriyar Manasse. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. 35 Jimillar maza daga mutanen Manasse 32,200 ne.
36 Daga zuriyar Benyamin. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. 37 Jimillar maza daga mutanen Benyamin 35,400 ne.
38 Daga zuriyar Dan. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. 39 Jimillar maza daga mutanen Dan 62,700 ne.
40 Daga zuriyar Asher. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. 41 Jimillar maza daga mutanen Asher 41,500 ne.
42 Daga zuriyar Naftali. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. 43 Jimillar maza daga mutanen Naftali kuwa 53,400 ne.
44 Waɗannan su ne mazan da Musa da Haruna, tare da shugabanni goma sha biyun nan na Isra’ila suka ƙidaya, kowa a madadin iyalinsa. 45 Dukan Isra’ilawan da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, an ƙidaya su bisa ga iyalansu. 46 Jimillar kuwa ita ce mutum 603,550.
47 Ba a dai ƙidaya zuriyar Lawi tare da saura kabilan ba. 48 Ubangiji ya riga ya gaya wa Musa cewa, 49 “Ka tabbatar ba ka ƙidaya mutanen Lawi ko kuma ka haɗe su tare a ƙidayan sauran Isra’ilawa ba. 50 A maimakon haka sai ka naɗa Lawiyawa su lura da tabanakul Shaida, wato, kan dukan kayayyaki da kuma kome da yake na wuri mai tsarki. Za su ɗauko tabanakul da dukan kayayyakinsa; za su lura da shi, su kasance kewaye da shi. 51 Duk sa’ad da za a gusar da tabanakul, Lawiyawa ne za su saukar da shi; kuma duk sa’ad da za a kafa shi, Lawiyawa ne za su yi haka. Duk wani dabam da ya je kusa da shi za a kashe shi. 52 Sauran Isra’ilawa za su zauna ƙungiya-ƙungiya, kowane mutum a ƙungiyarsa daidai bisa ga ƙa’idarsa. 53 Amma Lawiyawa za su kafa sansaninsu kewaye da tabanakul na Shaida. Don kada fushi yă fāɗo a kan al’ummar Isra’ilawa. Hakkin Lawiyawa ne su kula da tabanakul na Shaida.”
54 Isra’ilawa suka yi duk waɗannan kamar dai yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Ƙidaya 2 ->