6 Sai Yoshuwa ya sa musu albarka, ya sallame su, suka kuwa tafi gidajensu. 7 (Musa ya riga ya ba rabin kabilar Manasse gādo a Bashan; sauran rabin kabilar kuma Yoshuwa ya ba su gādo tare ’yan’uwansu a yammacin hayin Urdun.) Sa’ad da Yoshuwa ya sallame su su tafi gida, ya sa musu albarka, 8 ya ce, “Ku koma gidajenku tare da dukiya mai yawa, babban garken dabbobi, azurfa da zinariya, tagulla da ƙarfe, da tufafi masu yawa sosai, sai ku raba ganimar da kuka samu daga abokan gābanku, da ’yan’uwanku.”
9 Saboda haka sai mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse, suka bar Isra’ilawa a Shilo cikin Kan’ana don su koma Gileyad, ƙasarsu, wadda suka samu bisa ga umarnin Ubangiji ta wurin Musa.
10 Da suka kai Gelilot kusa da Urdun cikin ƙasar Kan’ana, sai mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse suka gina bagade a can, a Urdun. 11 Sa’ad da Isra’ilawa suka ji cewa sun gina bagade a iyakar Kan’ana, a Gelilot kusa da Urdun wajen gefensu na Isra’ilawa, 12 sai dukan Isra’ilawa suka taru a Shilo don su je su yaƙe su.
13 Saboda haka sai Isra’ilawa suka aiki Finehas ɗan Eleyazar, firist, zuwa ƙasar Gileyad, wurin mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse. 14 Suka aiki shugabanni guda goma su tafi tare da shi, ɗaya daga kowace kabilar Isra’ila, kowannensu shugaba ne a iyalansa.
15 Sa’ad da suka je Gileyad, wurin mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse, sai suka ce musu, 16 “Dukan jama’ar Ubangiji sun ce yaya za ku juya wa Allah na Isra’ila baya haka? Yaya za ku daina bin Ubangiji ku gina wa kanku bagade, ku yi masa tawaye yanzu? 17 Zunubin da Feyor ya yi bai ishe mu ba ne? Ga shi, har yanzu ba mu gama tsarkakewa daga wannan zunubi ba, ko da yake annoba ta auko wa mutanen Ubangiji! 18 Yanzu za ku daina bin Ubangiji ne?
21 Sai mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse suka amsa wa shugabannin iyalan Isra’ila suka ce, 22 “Maɗaukaki, Allah, Ubangiji! Maɗaukaki, Allah, Ubangiji ya sani! In mun yi wannan cikin tawaye ko rashin biyayya ga Ubangiji ne, kada ku bar mu da rai yau. 23 Idan mun bar bin Ubangiji, muka gina wa kanmu bagade don mu miƙa hadayun ƙonawa, ko kuwa hadayun gari, ko kuwa hadayun salama, to, bari Ubangiji kansa ya sāka mana.
24 “A’a! Mun yi haka ne don tsoro, kada nan gaba ’ya’yanku su ce wa ’ya’yanmu, ‘Me ya haɗa ku da Ubangiji, Allah na Isra’ila? 25 Ubangiji ya sa Urdun ya zama iyaka tsakaninmu da ku, ku mutanen Ruben da mutanen Gad! Ba ku da rabo cikin Ubangiji.’ ’Ya’yanku za su iya sa ’ya’yanmu su daina tsoron Ubangiji.
26 “Shi ya sa muka ce, ‘Bari mu yi shiri mu gina bagade, amma ba na ƙona hadayu ko na sadaka ba.’ 27 Sai dai yă zama shaida tsakaninmu da ku, da kuma waɗanda za su zo a baya, cewa za mu yi wa Ubangiji sujada a wurinsa mai tsarki, za mu miƙa hadayunmu na ƙonawa, hadayu na zumunta. Sa’an nan, nan gaba ’ya’yanku ba za su ce wa ’ya’yanmu, ‘Ba ku da rabo a cikin Ubangiji ba.’
28 “Muka kuma ce, ‘In har suka ce mana, ko ’ya’yanmu haka, sai mu amsa mu ce ku dubi bagaden da yake daidai da na Ubangiji wanda iyayenmu suka gina, ba don ƙona hadayu da kuma yin sadaka ba, sai dai don yă zama shaida tsakaninmu da ku.’
29 “Allah ya sawwaƙa mana mu tayar wa Ubangiji mu bar binsa, har mu gina bagade don miƙa hadayu na ƙonawa, da na gari, da na sadaka, ban da bagaden Ubangiji Allahnmu wanda yake tsaye a gaban tabanakul.”
30 Da Finehas firist, da shugabannin mutanen, shugabannin iyalan Isra’ila, suka ji abin da mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse suka ce, sai suka ji daɗi. 31 Sai Finehas ɗan Eleyazar, firist, ya ce wa mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse, “Yau mun san Ubangiji yana tare da mu, domin ba ku yi wa Ubangiji rashin aminci cikin wannan abu ba. Yanzu kun kuɓutar da Isra’ilawa daga hannun Ubangiji.”
32 Sai Finehas ɗan Eleyazar, firist, da shugabannin suka koma Kan’ana daga saduwa da mutanen Ruben da mutanen Gad a Gileyad, suka kai wa Isra’ilawa rahoto. 33 Isra’ilawa suka ji daɗin rahoton da suka ji, suka kuma yi wa Allah yabo. Ba su sāke yin maganar zuwa yaƙi don su rushe ƙasar da mutanen Ruben da mutanen Gad suke ciki ba.
34 Sai mutanen Ruben da mutanen Gad suka ba wa wannan bagaden sunan, Shaida Tsakaninmu, cewa Ubangiji Allah ne.
<- Yoshuwa 21Yoshuwa 23 ->