Link to home pageLanguagesLink to all Bible versions on this site
2
Rundunar fāra
1 Ku busa ƙaho a cikin Sihiyona;
ku yi karar amo a tsaunina mai tsarki.
 
Bari dukan mazaunan ƙasar su yi rawan jiki,
gama ranar Ubangiji tana zuwa.
Tana gab da faruwa
2 rana ce ta baƙin duhu ƙirin,
ranar gizagizai ce baƙi ƙirin.
Babbar rundunar mayaƙa mai ƙarfi tana zuwa
kamar ketowar alfijir a kan duwatsu
yadda ba a taɓa ganin irinta ba,
ba kuwa za a ƙara ganin irinta ba har tsararraki masu zuwa.
 
3 A gabansu wuta tana ci,
a bayansu ga harshen wuta yana ci,
A gabansu ƙasa ta yi kamar gonar Eden,
a bayansu kuma jeji ne wofi,
babu abin da ya kuɓuce musu.
4 Suna da kamannin dawakai;
suna gudu kamar dokin yaƙi.
5 Da motsi kamar na kekunan yaƙi
sun tsallake ƙwanƙolin duwatsu,
kamar ƙarar harshen wuta mai cin tattaka,
kamar runduna mai ƙarfi wadda ta ja dāgār yaƙi.
 
6 Da ganinsu, al’ummai sun kamu da azaba;
kowace fuska ta yanƙwane.
7 Sukan auka kamar jarumawa;
sukan hau katanga kamar sojoji.
Kowa yana takawa bisa ga tsari,
ba mai kaucewa.
8 Ba sa turin juna,
kowane yakan miƙe gaba.
Sukan kutsa cikin abokan gāba
ba mai tsai da su.
9 Sukan ruga cikin birni,
suna gudu a kan katanga.
Sukan hau gidaje,
sukan shiga ta tagogi kamar ɓarayi.
 
10 A gabansu duniya takan girgiza,
sararin sama kuma yakan jijjigu,
rana da wata su yi duhu,
taurari kuma ba sa ba da haske.
11 Ubangiji ya yi tsawa
wa shugaban mayaƙansa;
sojojinsa sun fi a ƙirge
masu ƙarfi ne kuma su waɗanda suke biyayya da umarninsa.
Ranar Ubangiji da girma take;
mai banrazana.
Wa zai iya jure mata?
Ku kyakkece zuciyarku
12 “Ko yanzu”, in ji Ubangiji,
“Ku juyo gare ni da dukan zuciyarku,
da azumi da kuka da makoki.”
 
13 Ku kyakkece zuciyarku
ba rigunanku ba.
Ku juyo ga Ubangiji Allahnku,
gama shi mai alheri ne mai tausayi kuma
mai jinkirin fushi da yawan ƙauna,
yakan kuma janye daga aika da bala’i.
14 Wa ya sani? Ko zai juya yă kuma ji tausayi
yă sa mana albarka
ta wurin hadaya ta gari da hadaya ta sha
wa Ubangiji Allahnku.
 
15 A busa ƙaho a Sihiyona,
a yi shelar azumi mai tsarki,
a kira tsarkakan taro.
16 A tattara mutane;
ku tsarkake taron;
ku kawo dattawa wuri ɗaya;
ku kuma tara yara,
da waɗanda suke shan mama.
Bari ango yă bar ɗakinsa
amarya kuma lolokinta.
17 Bari firistocin da suke yin hidima a gaban Ubangiji,
su yi kuka tsakanin filin haikali da bagade.
Bari su ce, “Ka cece mutanenka, ya Ubangiji.
Kada ka bar gādonka yă zama abin dariya,
da abin ba’a a cikin al’ummai.
Me zai sa a ce a cikin mutane, ‘Ina Allahnsu yake?’ ”
Amsar Ubangiji
18 Ta haka Ubangiji zai yi kishin ƙasarsa
yă kuma ji tausayin mutanensa.

19 Ubangiji zai amsa*Ko kuwa Ubangiji yă ji kishin / da kuma tausayawa / 19 Ubangiji ya amsa musu ya ce,

“Ina aika da hatsi, sabon ruwan inabi, da mai,
isashe da zai ƙosar da ku sosai;
ba kuma zan ƙara maishe ku
abin dariya ga al’ummai ba.
 
20 “Zan kori sojojin arewa nesa da ku,
in tura su cikin busasshiyar ƙasa marar amfani kuma,
kuma da sawunsu na gaba zan tura su zuwa gabashin tekuWato, Mediterraniyan.
da kuma sawunsu na baya tura su zuwa yammanci a Bahar Rum.wannan teku na Bahar Maliya ne
Warinsu kuma zai bazu;
ɗoyinsu zai tashi.”
 
Tabbatacce ya yi al’amura masu girma.§Ko kuwa ya tashi. Tabbatacce ya yi abubuwa masu girma
21 Kada ki ji tsoro, ya ƙasa;
ki yi murna ki kuma yi farin ciki.
Tabbatacce Ubangiji ya yi abubuwa masu girma.
22 Kada ku ji tsoro, ya ku namun jeji,
gama wuraren kiwo sun yi kore shar.
Itatuwa suna ba da ’ya’yansu;
itacen ɓaure da na inabi suna ba da amfaninsu.
23 Ku yi murna, ya ku mutanen Sihiyona,
ku yi farin ciki cikin Ubangiji Allahnku,
gama ya ba ku
ruwan bazara cikin adalci.*ko / mai koyar da gaskiya
Yakan aika muku yayyafi a yalwace,
na bazara da na kaka, kamar dā.
24 Masussukai za su cika da hatsi;
randuna za su cika da sabon ruwan inabi da mai suna zuba.
 
25 “Zan mayar muku da abin da fāra suka ci a waɗannan shekaru
waɗanda ɗango da fāra masu gaigayewa,
da kuma sauran fāra da tarin fāraTakamamme ma’anar kalmomin nan guda huɗu na Ibraniyancin da aka yi amfani da su a nan domin fāra babu wanda ya sani.
babban mayaƙan da na aika don su fāɗa muku.
26 Za ku sami a wadace ku ci, har sai kun ƙoshi,
za ku kuma yabi sunan Ubangiji Allahnku,
wanda ya yi muku ayyukan banmamaki;
mutanena ba za su ƙara shan kunya ba.
27 Sa’an nan za ku sani ina cikin Isra’ila,
cewa ni ne Ubangiji Allahnku,
babu wani kuma;
mutanena ba za su ƙara shan kunya ba.
Ranar Ubangiji
28 “Daga baya kuma,
zan zuba Ruhuna a bisan dukan mutane.
’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci,
tsofaffinku za su yi mafarkai,
matasanku za su ga wahayoyi.
29 Har ma a bisan bayina, maza da mata,
zan zuba Ruhuna a kwanakin nan.
30 Zan nuna abubuwan banmamaki a cikin sammai
da kuma a kan duniya,
za a ga jini da wuta da murtukewar hayaƙi.
31 Rana za tă duhunta
wata kuma yă zama jini
kafin isowar babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji.
32 Amma dukan waɗanda suka nemi
Ubangiji za su tsira.
Kamar yadda Ubangiji ya ce,
gama a Dutsen Sihiyona da Urushalima
akwai ceto,
a cikin waɗannan da Ubangiji ya kira.

<- Yowel 1Yowel 3 ->