37
1 “Wannan ya sa gabana ya fāɗi,
zuciyata ta yi tsalle.
2 Ka saurara! Ka saurari rurin muryarsa,
tsawar da take fita daga bakinsa.
3 Ya saki walƙiyarsa, a ƙarƙashin dukan sammai
ya kuma aika ta ko’ina a cikin duniya.
4 Bayan wannan sai ƙarar rurinsa ta biyo;
Ya tsawata da muryarsa mai girma.
Sa’ad da ya sāke yin tsawa
ba ya rage wani abu.
5 Muryar Allah tana tsawatawa a hanyoyi masu ban al’ajabi;
yana yin manyan abubuwa waɗanda sun wuce ganewarmu.
6 Yakan ce wa dusar ƙanƙara, ‘Fāɗo a kan duniya,’
ya kuma ce wa ruwa, ‘Zubo da ƙarfi.’
7 Domin dukan mutanen da ya halitta za su san aikinsa,
ya hana kowane mutum yin wahalar aiki.
8 Dabbobi sun ɓoye;
sun zauna cikin kogunansu.
9 Guguwa tana fitowa daga inda take,
sanyi kuma daga iska mai sanyi.
10 Da numfashinsa Allah yana samar da ƙanƙara
sai manyan ruwaye su zama ƙanƙara.
11 Yana cika gizagizai da lema;
yana baza walƙiyarsa ta cikinsu.
12 Bisa ga bishewarsa suke juyawa
a kan fuskar duniya,
suna yin dukan abin da ya
umarce su su yi.
13 Yana aiko da ruwa domin horon mutane,
ko kuma don yă jiƙa duniya yă kuma nuna ƙaunarsa.
14 “Ka saurari wannan Ayuba;
ka tsaya ka dubi abubuwan al’ajabi na Allah.
15 Ko ka san yadda Allah yake iko da gizagizai
ya kuma sa walƙiyarsa ta haskaka?
16 Ko ka san yadda gizagizai suke tsayawa cik a sararin sama,
waɗannan abubuwa al’ajabi na mai cikakken sani.
17 Kai mai sa kaya don ka ji ɗumi lokacin da
iska mai sanyi take hurawa,
18 ko za ka iya shimfiɗa sararin sama tare da shi
da ƙarfi kamar madubi?
19 “Gaya mana abin da ya kamata mu ce masa;
ba za mu iya kawo ƙara ba domin duhunmu.
20 Ko za a gaya masa cewa ina so in yi magana?
Ko wani zai nemi a haɗiye shi?
21 Yanzu ba wanda zai iya kallon rana,
yadda take da haske a sararin sama
bayan iska ta share ta.
22 Yana fitowa daga arewa da haske na zinariya,
Allah yana zuwa da ɗaukaka mai ban al’ajabi.
23 Maɗaukaki ya fi ƙarfin ganewarmu,
shi babban mai iko ne, mai gaskiya da babban adalci,
ba ya cutar mutum.
24 Saboda haka, mutane suke girmama shi,