3 Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ko ka ga bawana Ayuba? A cikin duniya babu wani kamar sa; shi marar laifi ne, adali kuma, mutum ne mai tsoron Allah ba ruwansa da mugunta. Kuma har yanzu bai fasa zama mai aminci ba duk da wahalar da ka sa na bari ka ba shi ba tare da wani dalili ba.”
4 Shaiɗan ya amsa ya ce, “Fata don fata! Mutum zai iya rabuwa da duk abin da yake da shi domin ransa. 5 Ka ɗan taɓa lafiyar jikinsa ka gani ba shakka zai la’anta ka kana ji kana gani.”
6 Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, duk abin da yake da shi yana hannunka, amma kada ka taɓa shi, shi kansa.”
7 Sai Shaiɗan ya bar Ubangiji, ya je ya sa wa Ayuba ƙuraje masu zafi a jikinsa daga tafin ƙafafunsa har zuwa kansa. 8 Sai Ayuba ya ɗauki kaskon tukunya yana ta sosa ƙurajen da shi, yayinda yake zaune cikin toka.
9 Matarsa ta ce masa, “Har yanzu kana nan da amincinka? Ka la’anta Allah ka mutu!”
10 Ya amsa ya ce, “Kina magana kamar wawiya. Alheri kaɗai za mu dinga samu daga Allah ban da wahala?”