Link to home pageLanguagesLink to all Bible versions on this site
17
1 Na karaya,
kwanakina sun kusa ƙarewa,
kabari yana jirana.
2 Ba shakka masu yi mini ba’a suna kewaye da ni;
idanuna suna ganin tsokanar da suke yi mini.
 
3 “Ya Allah, ka ba ni abin da ka yi mini alkawari.
Wane ne zai kāre ni?
4 Ka rufe zuciyarsu yadda ba za su iya ganewa ba,
saboda haka ba za ka bari su yi nasara ba.
5 In mutum ya juya wa abokansa baya don a ba shi wata lada
’ya’yansa za su makance.
 
6 “Allah ya sa na zama abin da kowa yake magana a kai
wanda kowa yake tofa wa miyau a fuska.
7 Idanuna ba sa gani sosai don baƙin ciki;
jikina ya zama kamar inuwa kawai
8 Mutanen da suke masu adalci wannan abu ya ba su tsoro;
marasa laifi sun tayar wa marasa tsoron Allah.
9 Duk da haka, masu adalci za su ci gaba da tafiya a kan hanyarsu,
waɗanda hannuwansu suke da tsabta kuma za su ƙara ƙarfi.
 
10 “Amma ku zo dukanku, ku sāke gwadawa!
Ba zan sami mutum ɗaya mai hikima ba a cikinku.
11 Kwanakina sun wuce, shirye-shiryena sun ɓaci
haka kuma abubuwan da zuciyata take so.
12 Mutanen nan sun juya rana ta zama dare.
A tsakiyar duhu suka ce, ‘Haske yana kusa.’
13 In kabari ne begen da nake da shi kaɗai,
in na shimfiɗa gadona a cikin duhu,
14 In na ce wa kabari, ‘Kai ne mahaifina,’
tsutsa kuma ke ce, ‘Mahaifiyata’ ko ‘’yar’uwata,’
15 To, ina begena yake?
Wane ne zai iya ganin wani bege domina?
16 Ko begena zai tafi tare da ni zuwa kabari ne?
Ko tare za a bizne mu cikin ƙura?”

<- Ayuba 16Ayuba 18 ->