Link to home pageLanguagesLink to all Bible versions on this site
12
Ayuba
1 Sai Ayuba ya amsa,
2 “Ba shakka ku ne mutanen nan,
hikima za tă mutu tare da ku!
3 Amma ni ma ina da hankali kamar ku;
ba ku fi ni ba.
Wane ne bai san duk waɗannan abubuwan ba?
 
4 “Na zama abin dariya ga abokaina,
ko da yake na yi kira ga Allah ya kuwa amsa mini,
duk da haka suka yi mini riya ko da yake ni mai adalci ne kuma marar laifi!
5 Mutanen da ba su da damuwa suna jin daɗin ganin waɗanda
suke dab da fāɗuwa.
6 Amma wurin zaman ’yan fashi yana nan ba mai damunsu,
waɗanda kuma suke saɓa wa Allah suna zamansu lafiya,
har ma da masu ɗaukar allahnsu a hannuwansu.
 
7 “Amma ka tambayi dabbobi, za su kuma koya maka,
ko kuma tsuntsayen sararin sama kuma za su gaya maka.
8 Ko ka yi magana da duniya, za tă kuma koya maka,
ko kuma ka bar kifin teku su sanar da kai.
9 Wane ne cikin waɗannan bai san
cewa hannun Ubangiji ne ya yi wannan ba?
10 Ran kowace halitta yana a hannunsa,
haka kuma numfashin dukan ’yan adam.
11 Ko kunne ba ya gwada kalmomi
kamar yadda harshe yake ɗanɗana abinci?
12 Ko ba a wurin tsofaffi ake samun hikima ba?
Ba tsawon rai yana kawo ganewa ba?
 
13 “Allah ne mai iko da kuma hikima,
shawara da ganewa nasa ne.
14 Abin da ya rushe ba a iya ginawa ba;
in ya kulle mutum ba a iya buɗe shi a sake shi ba.
15 Idan ya hana ruwan sama, za a yi fări;
in kuma ya saki ruwa za a yi ambaliya.
16 Shi ne mai ƙarfi da kuma mai nasara;
mai ruɗi da wanda aka ruɗa, duk nasa ne.
17 Yakan sa mashawarta su zama marasa hikima
yă kuma sa wawaye su zama masu shari’a.
18 Yana cire sarƙar da sarakuna suka ɗaura
yă kuma ɗaura musu wata tsumma a kwankwaso.
19 Yakan ƙasƙantar da firistoci
yă kuma tumɓuke masu ikon da aka kafa tun da daɗewa.
20 Yana sa amintattun mashawarta su yi shiru
yakan kawar da hikimar dattawa.
21 Yakan sa masu iko su ji kunya
yă kuma ƙwace ƙarfin masu ƙarfi.
22 Yana buɗe abubuwan da suke cikin duhu
yă kuma kawo haske a wuraren da ba haske;
23 yana sa al’ummai su zama manya, sai kuma yă hallaka su;
yana sa al’ummai su ƙasaita, yă kuma watsar da su.
24 Yana hana shugabannin duniya ganewa;
Ya bar su su yi ta makuwa, su ruɗe, su ɓata.
25 Suna lallube cikin duhu ba haske;
yă sa su yi ta tangaɗi kamar bugaggu.