7 Marar amfanin nan ya ce, “Ranka yă daɗe, ba ni da wanda zai taimaka yă sa ni a cikin tafkin sa’ad da aka motsa ruwan. Yayinda nake ƙoƙarin shiga, sai wani yă riga ni.”
8 Sai Yesu ya ce masa, “Tashi! Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.” 9 Nan take mutumin ya warke; ya ɗauki tabarmarsa ya yi tafiya.
11 Amma ya amsa ya ce, “Mutumin da ya warkar da ni shi ya ce mini, ‘Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.’ ”
12 Sai suka tambaye shi suka ce, “Wane ne wannan da ya ce maka ka ɗauke ta ka yi tafiya?”
13 Mutumin da aka warkar kuwa bai ma san ko wane ne ba ne, gama Yesu ya ɓace cikin taron da yake can.
14 Daga baya Yesu ya same shi a haikali ya ce masa, “Ga shi, ka warke. Ka daina yin zunubi, in ba haka ba wani abin da ya fi wannan muni zai iya samunka.” 15 Sai mutumin ya je ya gaya wa Yahudawa cewa Yesu ne ya warkar da shi.
19 Sai Yesu ya ba su wannan amsa cewa, “Gaskiya nake gaya muku, Ɗan ba ya iya yin kome da kansa; yana yin abin da ya ga Ubansa yake yi ne kawai, gama duk abin da Uban yake yi shi ne Ɗan ma yake yi. 20 Gama Uban yana ƙaunar Ɗan yana kuma nuna masa duk abin da yake yi. I, za ku kuwa yi mamaki, gama zai nuna masa abubuwan da suka fi waɗannan girma. 21 Gama kamar yadda Uban yake tā da matattu yake kuma ba su rai, haka ma Ɗan yake ba da rai ga wanda ya ga dama. 22 Bugu da ƙari, Uban ba ya hukunta kowa, sai dai ya danƙa dukan hukunci a hannun Ɗan, 23 don kowa yă girmama Ɗan kamar yadda yake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan ba ya girmama Uban, da ya aiko shi ke nan.
24 “Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ji maganata ya kuma gaskata da wanda ya aiko ni yana da rai madawwami ba za a kuma hukunta shi ba; ya riga ya ƙetare daga mutuwa zuwa rai. 25 Gaskiya nake gaya muku, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya zo sa’ad da matattu za su ji muryar Ɗan Allah waɗanda kuwa suka ji za su rayu. 26 Gama kamar yadda Uban yana da rai a cikinsa, haka ya sa Ɗan yă kasance da rai a cikin kansa. 27 Ya kuma ba shi iko yă hukunta domin shi Ɗan Mutum ne.
28 “Kada ku yi mamakin wannan, gama lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke cikin kaburbura za su ji muryarsa 29 su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta za su tashi zuwa ga rai, waɗanda kuma suka aikata mugunta za su tashi zuwa ga hukunci. 30 Ni kaɗai dai ba na iya yin kome, ina shari’a ne bisa ga abin da na ji. Shari’ata kuwa mai adalci ce. Gama ba na neman gamsar da kaina, sai dai in gamshi shi wanda ya aiko ni.
33 “Kun aika wajen Yohanna ya kuma yi shaida a kan gaskiya. 34 Ba cewa ina neman shaidar mutum ba ne; sai dai na faɗi haka ne domin ku sami ceto. 35 Yohanna fitila ne da ya ci ya kuma ba da haske, kun kuwa zaɓa ku ji daɗin haskensa na ɗan lokaci.
36 “Ina da shaidar da ta fi ta Yohanna ƙarfi. Gama aikin nan da Uba ya ba ni in kammala, wanda kuwa nake yi, yana ba da shaida cewa Uba ne ya aiko ni. 37 Uba da ya aiko ni kuwa kansa ya yi shaida game da ni. Ba ku taɓa jin muryarsa ko ganin siffarsa ba, 38 maganarsa kuwa ba ta zama a cikinku, gama ba ku gaskata da wanda ya aiko ni ba. 39 Kuna ta nazarin Nassosi da himma don kuna tsammani ta wurinsu ne kuna samun rai madawwami. Nassosin nan ne suke ba da shaida a kaina, 40 duk da haka kun ƙi zuwa wurina domin ku sami rai.
41 “Ni ba na neman yabon mutane, 42 na fa san ku. Na san cewa ba ku da ƙaunar Allah a cikin zukatanku. 43 Na zo a cikin sunan Ubana, ba ku kuwa karɓe ni ba; amma a ce wani dabam ya zo a cikin sunan kansa, za ku karɓe shi. 44 Ta yaya za ku gaskata in kuna neman yabon junanku, ba kwa kuwa yin ƙoƙarin neman yabon da yake zuwa daga Allah Makaɗaici?
45 “Kada fa ku yi tsammani zan yi ƙararku wurin Uba. Akwai mai yin ƙararku, shi ne Musa, wanda kuke dogara da shi. 46 Da a ce kun gaskata da Musa, da kun gaskata ni, domin ya rubuta game da ni. 47 Amma da yake ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, yaya za ku gaskata maganata?”
<- Yohanna 4Yohanna 6 ->- a Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da Betzata; waɗansu kuma suna da Betsaida ne a nan.
- b Waɗansu rubuce-rubucen hannu marar muhimmanci sosai suna da shanyayyu, kuma suka jira a motsa ruwaye. 4 Lokaci-lokaci mala’ikan Ubangiji yakan sauko ya motsa ruwaye. Mutum na farko da ya shiga tafkin bayan motsawa zai warke daga kowace cutar da yake da ita.