Link to home pageLanguagesLink to all Bible versions on this site
21
Yesu da kamun kifin banmamaki
1 Daga baya Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiransa, a bakin Tekun Tibariya.*Wato, Tekun Galili Ga yadda ya faru. 2 Siman Bitrus, Toma (wanda ake kira Didaimus), Natanayel daga Kana ta Galili, ’ya’yan Zebedi maza, da kuma waɗansu almajirai guda biyu suna tare. 3 Sai Siman Bitrus ya ce musu, “Za ni kamun kifi,” suka ce, “Za mu tafi tare da kai.” Saboda haka suka fita suka shiga jirgin ruwa, amma a daren nan ba su kama kome ba.

4 Da sassafe, sai ga Yesu tsaye a gaci, amma almajiran ba su gane cewa Yesu ne ba.

5 Sai ya ce musu, “Abokai, kuna da kifi kuwa?”

Suka amsa suka ce, “A’a.”

6 Ya ce musu, “Ku jefa abin kamun kifinku dama da jirgin ruwan, za ku samu.” Da suka yi haka, sai suka kāsa jawo abin kamun kifin saboda yawan kifi.

7 Sai almajirin da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, “Ai, Ubangiji ne!” Nan da nan da Siman Bitrus ya ji ya ce, “Ai, Ubangiji ne,” sai ya yafa mayafinsa (don dā ma ya tuɓe shi), ya fāɗa cikin ruwan. 8 Sauran almajiran kuwa suka bi shi cikin jirgin ruwan, janye da abin kamun kifin cike da kifi, don ba su da nisa daga gaci, wajen yadi ɗari ne. 9 Da suka sauka, sai suka ga garwashin wuta a can da kifi a kai, da kuma ’yan burodi.

10 Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifin da kuka kama yanzu.” 11 Sai Siman Bitrus ya hau ya jawo abin kamun kifin gaci. Ya cika da manyan kifi, 153, amma duk da yawansun nan abin kamun kifin bai tsintsinke ba. 12 Yesu ya ce musu, “Ku zo ku karya kumallo.” Ba wani daga cikin almajiran da ya yi karambanin tambayarsa, “Wane ne kai?” Sun san cewa Ubangiji ne. 13 Yesu ya zo, ya ɗauki burodin ya ba su, haka kuma kifin. 14 Wannan fa shi ne sau na uku da Yesu ya bayyana kansa ga almajiransa bayan an tashe shi daga matattu.

Yesu ya sāke tabbatar da Bitrus
15 Da suka gama ci, sai Yesu ya ce wa Siman Bitrus, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske fiye da waɗannan?”
Ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.”
Yesu ya ce, “Ciyar da ’ya’yan tumakina.”

16 Har wa yau Yesu ya ce, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske?”

Ya amsa ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.”
Yesu ya ce, “Lura da tumakina.”

17 Sau na uku ya ce masa, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata?”

Sai Bitrus ya ɓata rai saboda Yesu ya tambaye shi sau na uku, “Kana ƙaunata?” Ya ce, “Ubangiji ka san kome duka; ka san cewa, ina ƙaunarka.”
Yesu ya ce, “Ciyar da tumakina. 18 Gaskiya nake faɗa maka, sa’ad da kake saurayi kakan yi wa kanka sutura ka tafi inda ka so; amma sa’ad da ka tsufa za ka miƙa hannuwanka, wani dabam yă yi maka sutura yă kai ka inda ba ka so.” 19 Yesu ya faɗi wannan ne, don yă nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi yă ɗaukaka Allah. Sa’an nan ya ce masa, “Bi ni!”

20 Bitrus ya juya ya ga cewa almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana binsu. (Wannan ne ya jingina a jikin Yesu sa’ad da suke cin abincin yamman nan da ya ce, “Ubangiji wane ne zai bashe ka?”) 21 Da Bitrus ya gan shi sai ya ce, “Ubangiji, wannan fa?”

22 Yesu ya amsa ya ce, “Idan na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki? Kai dai bi ni.” 23 Saboda wannan, jita-jita ta bazu a cikin ’yan’uwa cewa wannan almajirin ba zai mutu ba. Amma fa Yesu bai ce ba zai mutu ba; shi dai ya ce, “In na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki?”

24 Wannan shi ne almajirin da ya ba da shaida a kan waɗannan abubuwa ya kuma rubuta su. Mun san cewa shaidarsa gaskiya ce.

25 Yesu ya yi waɗansu abubuwa da yawa kuma. Da a ce an rubuta kowannensu, na tabbata ko duniya duka ba za tă sami wuri saboda littattafan da za a rubuta ba.

<- Yohanna 20