Link to home pageLanguagesLink to all Bible versions on this site
47
Saƙo game da Filistiyawa
1 Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya annabi game da Filistiyawa kafin Fir’auna ya yaƙi Gaza.
 
2 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Dubi yadda ruwaye suna tasowa a arewa;
za su zama kogi mai rigyawa.
Za su malala a ƙasa da kuma a kan kome da yake cikinta,
garuruwa da waɗanda suke zaune a cikinsu.
Mutane za su yi kuka;
dukan mazaunan ƙasar za su yi kururuwa
3 da jin motsin takawar kofatan dawakai,
da jin surutun kekunan yaƙin abokin gāba
da motsin ƙafafunsu.
Ubanni ba za su juye don su taimaki ’ya’yansu ba;
hannuwansu za su yi laƙwas.
4 Gama rana ta zo
da za a hallaka Filistiyawa
a kuma datse dukan waɗanda suka ragu
waɗanda za su iya taimakon Taya da Sidon.
Ubangiji yana gab da hallaka Filistiyawa,
raguwa daga bakin tekun Kaftor.
5 Gaza za tă aske kanta cikin baƙin ciki;
Ashkelon zai yi shiru.
Ya raguwar da suke zama a fili,
har yaushe za ku tsattsage kanku?
 
6 “Za ku yi kuka kuna cewa, ‘Wayyo, takobin Ubangiji
sai yaushe za ka huta?
Ka koma kubenka;
ka huta, ka yi shiru.’
7 Amma ta yaya zai huta
sa’ad da Ubangiji ya umarta,
sa’ad da ya umarta shi
don yă faɗa wa Ashkelon da kuma bakin teku?”

<- Irmiya 46Irmiya 48 ->