5 Amma sojojin Babiloniyawa suka bi su, suka ci wa Zedekiya a filayen Yeriko. Suka kama shi suka kai shi wurin Nebukadnezzar a Ribla a ƙasar Hamat, inda aka yanke masa hukunci. 6 A can Ribla sarkin Babilon ya kashe ’ya’yan Zedekiya a idanunsa aka kuma kashe dukan manyan mutanen Yahuda. 7 Sa’an nan ya ƙwaƙule idanun Zedekiya ya kuma buga masa ƙuƙumi, ya kai shi Babilon.
8 Sai Babiloniyawa suka cinna wa fadar da kuma gidajen mutane wuta suka farfasa katangar Urushalima. 9 Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya kwashi mutanen da suka rage a birnin zuwa zaman bauta a Babilon, tare da waɗanda suka riga suka tafi wurinsa, da kuma sauran mutanen. 10 Amma Nebuzaradan shugaban matsaran ya bar waɗansu matalauta a ƙasar Yahuda, su da ba su da kome; a lokacin kuwa ya ba su gonakin inabi da kuma filaye.
11 To, fa, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya ba da wannan umarnai game da Irmiya ta wurin Nebuzaradan shugaban matsaran sarki cewa, 12 “Ka ɗauke shi ka lura da shi da kyau, kada ka yi masa wani mugun abu, amma ka yi masa dukan abin da yake so.” 13 Saboda haka Nebuzaradan shugaban matsara, Nebushazban babban hafsa, Nergal-Sharezer bafade mai girma da sauran hafsoshin sarkin Babilon 14 suka aika aka kawo Irmiya daga filin matsar. Suka miƙa shi ga Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, don yă kai shi gidansa. Saboda haka ya zauna a can a cikin mutanensa.
15 Yayinda aka kulle Irmiya a sansanin matsara, maganar Ubangiji ta zo masa cewa, 16 “Tafi ka faɗa wa Ebed-Melek mutumin Kush, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ina gab da cika maganata a kan wannan birni ta wurin masifa, ba wadata ba. A lokacin za tă cika a idanunka. 17 Amma zan kuɓutar da kai a wannan rana, in ji Ubangiji; ba zan ba da kai ga waɗanda kake tsoronsu ba. 18 Zan cece ka; ba za ka mutu ta wurin takobi ba amma za ka tsira da ranka, domin ka dogara gare ni, in ji Ubangiji.’ ”
<- Irmiya 38Irmiya 40 ->- a Ko kuwa Kwarin Urdun