6 “ ‘Duk da haka, zan kawo lafiya da warkarwa gare ta; zan warkar da mutanena in kuma wadata su da salama da zama lafiya. 7 Zan komo da Yahuda da Isra’ila daga bauta zan kuma sāke gina su kamar yadda suke a dā. 8 Zan tsarkake su daga dukan zunubin da suka yi mini zan kuma gafarta musu dukan zunubansu na yin mini tawaye. 9 Sa’an nan birnin nan za tă sa in zama sananne, farin ciki, yabo da girma a gaban dukan al’ummai a duniya da suka ji abubuwa masu kyau da na yi mata; za su kuma yi mamaki su kuma yi rawan jiki saboda yalwar wadata da salamar da na ba ta.’
10 “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Kuna cewa game da wannan wuri, “Kango ne, babu mutane ko dabbobi.” Duk da haka a cikin garuruwan Yahuda da titunan Urushalima da aka yashe, inda ba mutane ko dabbobi, za a sāke jin 11 sowa ta farin ciki da murna, muryoyin amarya da na ango, da muryoyin waɗanda suka kawo hadayun salama a gidan Ubangiji suna cewa,
12 “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, ‘A wannan wuri, kango da babu mutane ko dabbobi, cikin dukan garuruwansa za a sāke kasance da wurin kiwo don makiyaya su hutar da garkunansu. 13 A cikin garuruwan ƙasar tudu, garuruwan yammancin gindin dutse da na Negeb, a yankin Benyamin, a cikin ƙauyuka kewayen Urushalima da kuma a cikin garuruwan Yahuda, garkuna za su sāke bi a ƙarƙashin hannun mai ƙidayawa,’ in ji Ubangiji.
14 “ ‘Kwanaki suna zuwa,’ in ji Ubangiji, ‘sa’ad da zan cika alkawarin alheri da na yi wa gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda.
19 Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, 20 “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘In ka tā da alkawarina na rana da kuma alkawarina na dare, har dare da rana ba za su ƙara bayyana a ƙayyadaddun lokutansu ba, 21 to, sai a tā da alkawarina da Dawuda bawana da alkawarina da Lawiyawan da suke firistoci masu hidima a gabana, Dawuda kuma ba zai ƙara kasance da zuriyar da za tă yi mulki. 22 Zan sa zuriyar Dawuda bawana da kuma Lawiyawan da suke hidima a gabana su yi yawa kamar taurarin sararin sama da kuma yashin bakin tekun da ba a iya ƙidaya.’ ”
23 Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, 24 “Ba ka lura ba cewa waɗannan mutane suna cewa, ‘Ubangiji ya ƙi masarautai[a] biyu da ya zaɓa’? Saboda haka suka rena mutanena ba sa ƙara ɗaukansu a matsayin al’umma. 25 Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘In ban kafa alkawarina game da rana da kuma game da dare ba in kuma gyara dokokin sama da duniya ba, 26 to zan ƙi zuriyar Yaƙub da na Dawuda bawana ba zan kuma zaɓi ɗaya daga cikin ’ya’yansa maza ya yi mulki a kan zuriyar Ibrahim, Ishaku da Yaƙub ba. Gama zan mayar da wadatarsu[b] in kuma yi musu jinƙai.’ ”
<- Irmiya 32Irmiya 34 ->