23 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa, “Sa’ad da na komo da su daga bauta mutane a ƙasar Yahuda da cikin garuruwanta za su sāke yi amfani da waɗannan kalmomi. ‘Ubangiji ya albarkace ka, ya mazauni mai adalci, ya tsarkakan dutse.’ 24 Mutane za su zauna tare a Yahuda da dukan garuruwansa, manoma da waɗanda suke yawo da garkunansu. 25 Zan wartsake waɗanda suka gaji in kuma ƙosar da waɗanda ransu ya yi yaushi.”
26 A kan wannan na farka na duba kewaye. Barcina ya yi mini daɗi.
27 “Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan kafa gidan Isra’ila da gidan Yahuda da ’ya’yan mutane da na dabbobi. 28 Kamar yadda na lura da su don su tumɓuke su kuma rusar, su lalatar, su hallaka su kuma kawo masifa, haka zan lura da su don su gina su kuma dasa,” in ji Ubangiji. 29 “A waɗannan kwanaki mutane ba za su ƙara ce,
“ ‘Ubanni suka ci ’ya’yan inabi masu tsami,
haƙoran ’ya’ya suka mutu ba.’
30 A maimako, kowa zai mutu saboda zunubinsa; duk wanda ya ci ’ya’yan inabi masu tsami, haƙoransa ne za su mutu.
31 “Lokaci yana zuwa,” in ji Ubangiji,
“sa’ad da zan yi sabon alkawari
da gidan Isra’ila
da kuma gidan Yahuda.
32 Ba zai zama kamar alkawarin
da na yi da kakanni kakanninsu ba
sa’ad da na kama su da hannu
na bishe su daga Masar,
domin sun take alkawarina,
ko da yake na zama miji a gare su,”
in ji Ubangiji.
33 “Ga alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila
bayan wannan lokaci,” in ji Ubangiji.
“Zan sa dokata a tunaninsu
in kuma rubuta ta a zukatansu.
Zan zama Allahnsu,
za su kuma zama mutanena.
34 Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabci ba,
ko ya koya wa ɗan’uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji,’
domin duk za su san ni,
daga ƙaraminsu har zuwa babba,”
in ji Ubangiji.
“Gama zan gafarta muguntarsu
ba zan kuwa ƙara tuna da zunubansu ba.”
35 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
shi da ya kafa rana
don tă yi haske a yini
shi da ya sa wata da taurari
su yi haske da dare,
shi da yake dama teku
don raƙuman ruwansa su yi ruri
Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.
36 “In dai wannan kafaffiyar ƙa’ida ta daina aiki a gabana,”
in ji Ubangiji,
“to, sai zuriyar Isra’ila ta daina
zama al’umma a gabana.”
37 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“In a iya auna sammai
a kuma bincike tushen duniya a ƙarƙas
to, sai in ƙi dukan zuriyar Isra’ila ke nan
saboda dukan abin da suka yi,”
in ji Ubangiji.
38 “Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da za a sāke gina wannan birni domina daga Hasumiyar Hananel zuwa Ƙofar Kusurwa. 39 Ma’auni zai miƙe daga can ya nausa kai tsaye zuwa tudun Gareb sa’an nan ya juya zuwa Gowa. 40 Dukan kwarin da ake zubar da toka da kuma gawawwaki, da dukan lambatun da suke can har zuwa Kwarin Kidron a gabas zuwa kusurwar Ƙofar Doki, za su zama mai tsarki ga Ubangiji. Ba za a ƙara tumɓuke birnin ko a rushe shi ba.”