5 Ku saurara, ’yan’uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi waɗanda suke matalauta a idon duniya don su zama masu wadata cikin bangaskiya, su kuma gāji mulkin da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba? 6 Ga shi kun wulaƙanta matalauta. Ashe, ba masu arziki ne suke cutarku ba? Ba su ba ne suke jan ku zuwa kotu? 7 Ba su ba ne suke ɓata sunan nan mai martaba wanda aka san ku da shi ba?
8 In fa kun kiyaye dokan nan ta mulki wadda take cikin Nassi mai cewa, “Ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,”[a] kun yi daidai. 9 Amma in kuka nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan shari’a kuma ta same ku da laifi a matsayin masu karya doka. 10 Gama duk wanda ya kiyaye dukan doka amma ya yi tuntuɓe a kan abu ɗaya kaɗai, ya zama mai laifin karya dukansu ke nan. 11 Gama shi da ya ce, “Kada ka yi zina,”[b] shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisankai.”[c] In kuwa ba ka zina amma kana kisankai, ka zama mai karya doka ke nan.
12 Ku yi magana ku kuma yi aiki kamar waɗanda za a yi musu shari’a bisa ga doka mai ba da ’yanci, 13 gama za a yi wa duk wanda bai nuna jinƙai ba hukunci babu jinƙai. Jinƙai yakan yi nasara a kan hukunci!
18 Amma wani zai ce, “Kai kana da bangaskiya; ni kuma ina da ayyuka.”
20 Kai wawa, kana son tabbaci cewa bangaskiya marar ayyuka banza ce? 21 Ashe, ba a mai da kakanmu Ibrahim mai adalci saboda abin da ya yi ba ne sa’ad da ya miƙa ɗansa Ishaku a bisa bagade? 22 Ai, ka gani cewa bangaskiyarsa da ayyukansa sun yi aiki tare, bangaskiyarsa kuma ta zama cikakkiya ta wurin abin da ya yi. 23 Aka kuma cika nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne gare shi,”[d] aka kuma ce da shi abokin Allah. 24 Kun ga cewa ashe mutum zai sami kuɓuta ta wurin abin da ya yi ne ba ta wurin bangaskiya kaɗai ba.
25 Ta haka kuma ashe, Rahab karuwan nan ba a ɗauke ta mai adalci ce saboda abin da ta yi ba ne sa’ad da ta ba wa ’yan leƙen asirin nan masauƙi ta kuma sallame su suka tafi ta wata hanya dabam? 26 Kamar yadda jikin da babu ruhu matacce ne, haka ma bangaskiyar da babu ayyuka matacciya ce.
<- Yaƙub 1Yaƙub 3 ->