1Ubangiji ya ce mini, “Ka ɗauki naɗaɗɗen littafi mai girma ka yi rubutu a kai da alƙalami kurum, Maher-Shalal-Hash-Baz.[a]2 Zan kuma kira Uriya firist da Zakariya ɗan Yeberekiya su zama mini amintattun shaidu.”
3 Sa’an nan na tafi na yi jima’i da annabiya, ta kuwa yi ciki ta haifi ɗa. Ubangiji kuma ya ce mini, “Raɗa masa suna, Maher-Shalal-Hash-Baz. 4 Kafin yaron yă san yadda zai ce ‘Babana’ ko ‘Mamana,’ sarkin Assuriya zai kwashe arzikin Damaskus da ganimar Samariya.”
11Ubangiji ya yi mini magana da hannunsa mai ƙarfi a kaina, yana yi mini gargaɗi kada in bi hanyar waɗannan mutane. Ya ce,
12 “Kada ka kira wani abu makirci
game da kome da waɗannan mutane suke kira makirci;[e]
kada ji tsoron abin da suke tsoro,
kada kuma ka firgita game da shi.
13Ubangiji Maɗaukaki shi ne za ka ɗauka a matsayi mai tsarki,
shi ne wanda za ka ji tsoro,
shi ne za ka yi rawar jiki a gabansa,
14 zai kuwa kasance a wuri mai tsarki;
amma ga dukan gidajen Isra’ila zai zama
dutsen da zai sa mutane su yi tuntuɓe
dutse kuma da zai sa su fāɗi.
Ga dukan mutanen Urushalima kuma zai zama
tarko da raga.
15 Yawancinsu za su yi tuntuɓe;
za su fāɗi a kuwa ragargaza su,
za a sa musu tarko a kuma kama su.”
16 Ɗaura shaidar nan ta gargadi
ka kuma yimƙe umarnin Allah a cikin almajiraina.
17 Zan saurari Ubangiji,
wanda ya ɓoye fuskarsa daga gidan Yaƙub.
Zan dogara gare shi.
18 Ga ni, da yaran da Ubangiji ya ba ni. Mu alamu ne da shaidu a cikin Isra’ila daga Ubangiji Maɗaukaki, wanda yake zama a Dutsen Sihiyona.
19 Sa’ad da mutane suka ce muku ku nemi shawarar ’yan bori da masu sihiri, waɗanda suke shaƙe murya har ba a jin abin da suke faɗi, bai kamata mutane su nemi shawara daga Allahnsu ba? Me zai sa ku nemi shawara daga matattu a madadin masu rai? 20 Nemi umarnin Allah da kuma shaidar jan kunne. Duk wanda bai yi magana bisa ga wannan kalma ba, ba su da amfani. 21 Cikin matsuwa da yunwa, za su yi ta kai komo ko’ina a ƙasar; sa’ad da suka ji yunwa, za su yi fushi su tā da idanu sama, su zagi sarkinsu da Allahnsu. 22 Sa’an nan za su zura wa ƙasa idanu, abin da za su gani kawai shi ne matsuwa da duhu da kuma abin banrazana, za a kuma jefa su cikin baƙin duhu.