Link to home pageLanguagesLink to all Bible versions on this site
56
Ceto domin waɗansu
1 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Ku riƙe gaskiya
ku yi abin da yake daidai,
gama cetona yana kusa
za a kuma bayyana adalcina nan da nan.
2 Mai albarka ne mutumin da ya aikata wannan,
mutumin da ya riƙe kam
yana kiyaye Asabbaci ba tare da ƙazantar da shi ba,
yana kuma kiyaye kansa daga yin mugun abu.”
 
3 Kada baƙon da ya miƙa kansa ga Ubangiji ya ce,
“Ai Ubangiji zai ware ni daga mutanensa.”
Kada kuma wani bābā ya yi gunaguni cewa,
“Ni busasshen itace ne kawai.”

4 Gama ga abin da Ubangiji ya faɗa,

“Wa bābānnin da suna kiyaye Asabbatai,
waɗanda suka zaɓi yin abin da ya gamshe ni
suna kuma riƙe da alkawarina kankan,
5 a gare su cikin haikalina da kuma bangayensa
zan ba da matuni da kuma suna
mafi kyau fiye da ’ya’ya maza da kuma ’ya’ya mata;
zan ba su madawwamin sunan
da ba za a raba su da shi ba.
6 Baƙin da suka miƙa kansu ga Ubangiji
don su bauta masa,
su kuma ƙaunaci sunan Ubangiji,
waɗanda kuma suke yin masa sujada,
duk waɗanda suka kiyaye Asabbaci ba tare da ƙazantar da shi ba
suka kuma riƙe alkawarina kankan,
7 waɗannan ne zan kai tsattsarkan dutsena
in sa su yi farin ciki a gidana na addu’a.
Hadayunsu na ƙonawa da sadakokinsu
za su zama abin karɓa a bagadena;
gama za a ce da gidana
gidan addu’a domin dukan al’ummai.”
8 Ubangiji Mai Iko Duka ya furta cewa,
zai tattara korarru na Isra’ila,
“Zan ƙara tattaro waɗansu
bayan waɗanda na riga na tattara.”
Zargin da Allah ya yi a kan mugaye
9 Ku zo, dukanku namun jeji,
ku zo ku ci, dukanku namun jeji!
10 Matsaran Isra’ila makafi ne,
dukansu jahilai ne;
dukansu bebayen karnuka ne
ba za su iya haushi ba;
suna kwance ne kawai suna mafarki,
suna son barci ba dama.
11 Su karnuka ne masu kwaɗayi;
ba su taɓa ƙoshi.
Su makiyaya ne marasa ganewa;
duk sun nufi inda suka ga dama,
kowa yana nemar wa kansa riba.
12 Kowanne yakan ce, “Zo, bari in samo ruwan inabi!
Bari mu cika cikinmu da barasa!
Gobe ma zai zama kamar yau,
ko ma fiye da haka.”