6
Isra’ila marar tuba
1 “Ku zo, mu koma ga Ubangiji.
Ya yayyage mu kucu-kucu
amma zai warkar da mu;
ya ji mana ciwo
amma zai daure mana miyakunmu.
2 Bayan kwana biyu zai rayar da mu,
a rana ta uku zai tashe mu,
don mu rayu a gabansa.
3 Bari mu yarda da Ubangiji;
bari mu nace gaba don mu yarda da shi.
Muddin rana tana fitowa,
zai bayyana;
zai zo mana kamar ruwan bazara,
kamar ruwan saman farko da yake jiƙe ƙasa.”
4 “Me zan yi da kai Efraim?
Me zan yi da kai Yahuda?
Ƙaunarku tana kamar hazon safiya,
kamar raɓar safiya da takan ɓace.
5 Saboda haka na yayyaga ku kucu-kucu tare da annabawana,
na kashe ku da kalmomin bakina;
hukuntaina sun haskaka kamar walƙiya a kanku.
6 Gama jinƙai nake bukata, ba hadaya ba,
ku kuma san Allah a maimakon hadayun ƙonawa.
7 Kamar Adamu, sun tā da alkawari,
sun yi mini rashin aminci a can.
8 Gileyad birni ce ta mugayen mutane,
da tabon alamun jini.
9 Kamar yadda mafasa sukan yi fakon mutum,
haka ƙungiyoyin firistoci suke;
suna kisa a hanya zuwa Shekem,
suna aikata laifofi bankunya.
10 Na ga wani abu mai bantsoro
a gidan Isra’ila.
A can Efraim ya miƙa wuya ga karuwanci
Isra’ila kuma ta ƙazantu.
11 “Ku kuma, ya mutanen Yahuda,
na shirya muku ranar girbi.