6 Sa’ad da aka shirya kome haka, sai firistoci suka shiga kullum cikin ɗaki na waje don su yi hidimarsu. 7 Amma babban firist ne kaɗai yakan shiga ɗaki na ciki-ciki, sau ɗaya tak a shekara, kuma sai da jini, wanda yakan miƙa domin zunubansa da kuma domin zunuban da mutane suka yi a cikin rashin sani. 8 Ta haka Ruhu Mai Tsarki ya nuna cewa ba a riga an bayyana hanyar shiga Wuri Mafi Tsarki ba tukuna, muddin tabanakul na fari yana nan tsaye. 9 Wannan ma yana da ma’ana wa mutane a yau. Ya nuna cewa ba za mu iya wanke lamirinmu ta wurin miƙa baye-baye da hadayu ba. 10 Waɗannan ƙa’idodi sun shafi sha’anin abinci da abin sha ne kawai da kuma ƙa’idodi tsarkake kanmu. Dokoki game da abubuwa na waje da ake amfani da su za su kasance ne sai lokacin ya yi da za a kawo abu mafi kyau.
15 Saboda haka Kiristi shi ne matsakancin sabon alkawari, don waɗanda aka kira su sami madawwamin gādon da aka yi alkawari, yanzu da ya mutu a matsayin mai fansa don yă ’yantar da su daga zunuban da aka aikata a ƙarƙashin alkawari na farko.
16 Sa’ad da wani ya yi alkawari game da gādonsa,[b] dole a tabbatar da mutuwar wanda ya yi ta, 17 domin alkawarin gādo yana aiki ne kawai bayan mai yinsa ya mutu, ba ya taɓa aiki yayinda mai yinsa yana da rai. 18 Shi ya sa alkawari na farko bai fara aiki ba sai da aka zub da jini. 19 Sa’ad da Musa ya sanar wa dukan mutane kowane umarni na doka, sai ya ɗauki jinin maruƙa tare da ruwa, jan ulu da kuma rassan hizzob, ya yayyafa a kan naɗaɗɗen littafin da kuma a kan dukan mutanen. 20 Ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Allah ya umarce ku ku kiyaye.”[c] 21 Ta haka ya yayyafa jinin a kan tabanakul da kuma a kan dukan kayayyakin da ake amfani da su don yin hidima. 22 Tabbatacce, doka ta bukaci a tsabtacce kusa kowane abu da jini, kuma in ba tare da zub da jini ba babu gafara.
23 Waɗannan abubuwa hotuna ne kawai na abin da yake a sama, dole kuma a tsarkake su ta wurin waɗannan ƙa’idodi. Amma dole a tsarkake ainihin abubuwa na sama da wani abu mafi kyau. 24 Gama Kiristi bai shiga wani wuri tsattsarka da mutum ya yi ba, wanda yake hoto ne kawai na gaskataccen, a’a sama kanta ya shiga, domin yă bayyana a gaban zatin Allah a yanzu saboda mu. 25 Bai kuwa shiga sama domin yă yi ta miƙa kansa a kai a kai, yadda babban firist yake shiga Wuri Mafi Tsarki kowace shekara da jinin da ba nasa ba. 26 Da a ce haka ne, ai, da Kiristi ya sha wahala sau da yawa tun halittar duniya. Amma yanzu ya bayyana sau ɗaya tak a ƙarshen zamanai domin yă kawar da zunubi ta wurin miƙa kansa hadaya. 27 Kamar dai yadda aka ƙaddara wa mutum yă mutu sau ɗaya, bayan haka kuma sai shari’a, 28 haka aka miƙa Kiristi hadaya sau ɗaya domin yă ɗauke zunuban mutane masu yawa; zai kuma bayyana sau na biyu, ba don yă ɗauki zunubi ba, sai dai don yă kawo ceto ga waɗanda suke jiransa.
<- Ibraniyawa 8Ibraniyawa 10 ->