4 Aure yă zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci. 5 Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce,
7 Ku tuna da shugabanninku, waɗanda suka faɗa muku maganar Allah. Ku dubi irin rayuwar da suka yi ku kuma yi koyi da bangaskiyarsu. 8 Yesu Kiristi ba ya sākewa, shi ne a jiya, shi ne a yau, shi ne kuma har abada.
9 Kada a ɗauke muku hankali da sababbin koyarwa dabam-dabam. Yana da kyau zukatanmu su ƙarfafa ta wurin alheri, ba ta wurin abinci waɗanda ba su da amfani ga waɗanda suke cinsu. 10 Muna da bagade inda firistocin da suka yi hidima a tabanakul ba su da izini su ci.
11 Babban firist yakan ɗauki jinin dabbobi yă shiga cikin Wuri Mafi Tsarki a matsayin hadaya ta zunubi, amma jikunan dabbobin akan ƙone su a bayan sansani. 12 Haka ma Yesu ya sha wahala a bayan gari don yă tsarkake mutane ta wurin jininsa. 13 Saboda haka, sai mu fita mu je wajensa a bayan sansani, muna ɗaukar kunyar da ya sha. 14 Gama a nan ba mu da dawwammamen birni, sai dai muna zuba ido a kan birnin nan mai zuwa.
15 Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah, yabon leɓuna da yake shaidar sunansa. 16 Kada kuma ku manta yin aikin nagari da kuma taimakon waɗansu, gama da irin waɗannan hadayu ne Allah yake jin daɗi.
17 Ku yi wa shugabanninku biyayya ku kuma miƙa kanku ga ikonsu. Suna lura da ku kuma za su ba da lissafi a gaban Allah. Saboda haka kada ku sa su yi fushi saboda aikinsu, ku sa su yi farin ciki. In ba haka ba za su iya taimakonku ba ko kaɗan.
18 Ku yi mana addu’a. Mun tabbata cewa muna da lamiri mai kyau, kuma muna da marmari mu yi rayuwa ta bangirma a ta kowace hanya. 19 Ni musamman, ina roƙonku ku yi addu’a, don a komo da ni a gare ku ba da daɗewa ba.