6 Yanzu Isuwa ya san cewa Ishaku ya albarkaci Yaƙub ya kuma aike shi zuwa Faddan Aram don yă auri mata daga can, ya kuma san cewa sa’ad da ya albarkace shi, ya umarce shi cewa, “Kada ka auro wata mace daga cikin Kan’aniyawa,” 7 ya kuma san cewa Yaƙub ya yi biyayya da mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa, ya kuwa tafi Faddan Aram. 8 Sai Isuwa ya gane cewa matan Kan’aniyawa ba su gamshi mahaifinsa Ishaku ba; 9 saboda haka sai ya tafi wurin Ishmayel ya auri Mahalat, ’yar’uwar Nebayiwot da kuma ’yar Ishmayel ɗan Ibrahim, ban da matan da yake da su.
16 Sa’ad da Yaƙub ya farka daga barci, sai ya yi tunani ya ce, “Tabbatacce Ubangiji yana a wannan wuri, ban kuwa sani ba.” 17 Ya ji tsoro, ya kuma ce, “Wane irin wuri ne mai banrazana haka! Lalle wannan gidan Allah ne, kuma nan ne ƙofar sama.”
18 Kashegari da sassafe, sai Yaƙub ya ɗauki dutsen da ya yi matashin kai da shi, ya kafa shi al’amudi, ya kuma zuba mai a kansa. 19 Ya kira wannan wuri Betel†Betel yana nufin gidan Allah. ko da yake dā ana kiran birnin Luz ne.
20 Sa’an nan Yaƙub ya yi alkawari cewa, “In Allah zai kasance tare da ni yă kuma lura da ni a wannan tafiya, yă kuma ba ni abinci in ci da tufafi in sa, 21 har in dawo lafiya zuwa gidan mahaifina, to, Ubangiji‡Ko kuwa Da yake Allah… gidan mahaifina, Ubangiji zai zama Allahna 22 kuma§Ko kuwa gida, Ubangiji, kuwa zai zama Allahna, sa’an nan. 22 Kuma wannan dutsen da na kafa al’amudi, zai zama gidan Allah, kuma dukan abin da ka ba ni zan ba ka kashi ɗaya bisa goma.”
<- Farawa 27Farawa 29 ->- a Ko kuwa gaishe
- b Wato, arewa maso gabashin Mesofotamiya, haka ma a ayoyi 5, 6 da 7
- c Da Ibraniyanci El-Shaddai.
- d Ko tsani.
- e Ko kuwa can kusa da shi
- f Betel yana nufin gidan Allah.
- g Ko kuwa Da yake Allah… gidan mahaifina, Ubangiji
- h Ko kuwa gida, Ubangiji, kuwa zai zama Allahna, sa’an nan. 22 Kuma