3 Ya ce, “Ranka yă daɗe, in na sami tagomashi daga gare ku kada ku wuce bawanku. 4 Bari a kawo ruwa ku wanke ƙafafunku, ku huta a ƙarƙashin wannan itace. 5 Bari in samo muku wani abu ku ci don ku wartsake, sa’an nan ku ci gaba da tafiyarku; da yake kun biyo wurin bawanku.”
6 Saboda haka Ibrahim ya ruga zuwa wurin Saratu a cikin tenti ya ce, “Yi sauri, ki shirya mudu uku na gari mai laushi, ki cuɗa shi, ki yi burodi.”
7 Sa’an nan Ibrahim ya yi gudu zuwa garkensa, ya zaɓi ɗan maraƙi ya ba wa bawansa, bawansa kuma ya yi sauri ya gyara shi. 8 Sa’an nan Ibrahim ya ɗauko dambu da madara da naman ɗan maraƙin da aka gyara, ya kawo a gabansu. Yayinda suke ci, ya tsaya a gindin itace kusa da su.
9 Sai suka ce masa, “Ina Saratu matarka?”
10 Sa’an nan ɗayansu ya ce, “Lalle zan komo wurinka war haka shekara mai zuwa. Saratu matarka kuwa za tă haifi ɗa.”
13 Sai Ubangiji ya ce wa Ibrahim, “Me ya ba Saratu dariya har da ta ce, ‘Har zan iya haifi ɗa duk ta tsufata yanzu?’ 14 Akwai abin zai gagari Ubangiji? Zan komo wurinka a ƙayyadadden lokacin nan shekara mai zuwa kuma Saratu za tă haifi ɗa.”
15 Saratu ta ji tsoro, don haka sai ta yi ƙarya ta ce, “Ban yi dariya ba.”
20 Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Kuka a kan Sodom da Gomorra ta yi yawa, zunubinsu kuma ya yi muni sosai, 21 zan gangara in ga ko abin da suka yi ya yi muni kamar yadda kukan ya zo gare ni, zan bincike.”
22 Sai mutanen suka juya suka nufi wajen Sodom amma Ibrahim ya ci gaba da kasance a gaban Ubangiji.[b] 23 Sai Ibrahim ya matso wurinsa ya ce, “Za ka hallaka masu adalci tare da masu mugunta? 24 Me zai faru in akwai mutum hamshin masu adalci a cikin birnin? Ashe, za ka hallaka shi, ba za ka cece wurin saboda mutane hamsin nan masu adalcin da suke a cikinsa ba? 25 Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba, ka kashe masu adalci tare da masu mugunta, ka ɗauka masu adalci da masu mugunta daidai? Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba! Mai hukuncin dukan duniya ba zai aikata gaskiya ba?”
26 Ubangiji ce, “In na sami mutum hamshin masu adalci a cikin birnin Sodom, zan bar dukan birnin saboda su.”
27 Sai Ibrahim ya ƙara cewa, “Yanzu da na yi karambani har na yi magana da Ubangiji, ko da yake ni ba kome ba ne illa turɓaya da toka, 28 in yawan masu adalci sun kāsa hamshin da mutum biyar fa? Za ka hallaka dukan birnin saboda rashin mutum biyar ɗin?”
29 Ya sāke cewa, “In mutum arba’in kaɗai aka samu a can fa?”
30 Sai ya ce, “Kada Ubangiji ya yi fushi, amma bari in ƙara magana. A ce mutum talatin kaɗai aka samu a can fa?”
31 Ibrahim ya ce, “Yanzu fa da na yi karambani har na yi magana da Ubangiji, in ashirin kaɗai aka samu a can fa?”
32 Sa’an nan Ibrahim ya ce, “Kada Ubangiji yă yi fushi, amma bari in ƙara magana sau ɗaya tak. In aka sami mutum goma kaɗai a can fa?”
33 Sa’ad da Ubangiji ya gama magana da Ibrahim, ya tafi, Ibrahim kuma ya koma gida.
<- Farawa 17Farawa 19 ->