6 “ ‘Za ka ba wa birnin fāɗin mallakarsa kamu 5,000, tsawonsa kuma 25,000, haɗe da tsattsarkan rabo; zai kasance na gidan Isra’ila duka.
7 “ ‘Sarki zai kasance da fili da ya yi iyaka da kowane gefe na yankin wuri mai tsarki da kuma mallakar birnin. Zai miƙe ya yi wajen yamma daga gefen yamma ya kuma yi wajen gabas daga gefen gabas, yana miƙewa a tsawo daga wajen yamma zuwa wajen gabashin iyaka don yă yi hannun riga da rabon kabilan. 8 Wannan fili zai zama mallakarsa a Isra’ila. Kuma sarakunana ba za su ƙara zaluntar mutanena ba amma za su bar gidan Isra’ila ya mallaki ƙasar bisa ga kabilansu.
9 “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko na ce ku sarakunan Isra’ila, danniya da zaluncin da kuke yi sun isa! Ku yi shari’a bisa ga gaskiya da adalci, ku bar korar mutanena, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. 10 Ku yi amfani da garwan da yake daidai, efa[a] da yake daidai da kuma garwa[b] da yake daidai. 11 Efa da garwan su kasance girmansu ɗaya, garwan ya zama kashi ɗaya bisa goma na ganga[c] efa kuma ya zama kashi ɗaya bisa goma na ganga; ganga fitaccen ma’auni na duka biyu. 12 Shekel zai kasance da gera ashirin. Shekel ashirin a haɗa da shekel ashirin da biyar a haɗa da shekel goma sha biyar zai zama mina guda.[d]
18 “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a farkon wata a rana ta fari za ku ba da ɗan bijimi marar lahani a kuma tsarkake wuri mai tsarki. 19 Firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubi ya shafa a madogaran ƙofar haikali, a kusurwoyi huɗu na gefen bisa na bagade da kuma a kan madogaran ƙofar shiga na fili na can ciki. 20 Za ku yi haka kuma a rana ta bakwai ga watan domin duk wanda ya yi zunubai ba da gangan ba ko ta wurin rashin sani; saboda haka sai ku yi kafara domin haikalin.
21 “ ‘A wata na fari a rana ta goma sha huɗu za ku kiyaye Bikin Ƙetarewa, bikin da yakan ɗauki kwana bakwai, a lokacin ne za ku riƙa cin burodi marar yisti. 22 A wannan rana sarki zai tanada bijimi a matsayin hadaya don zunubi domin kansa da kuma domin dukan mutanen ƙasar. 23 Kowace rana a kwanaki bakwai na Bikin zai tanada bijimai guda bakwai da raguna bakwai marar lahani a matsayi hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, da kuma bunsuru saboda hadaya don zunubi. 24 Zai tanada efa na gari don kowane bijimi da kuma efa don kowane rago, tare da kwalabar mai don kowane efa guda.
25 “ ‘A lokacin kwana bakwai na Bikin, waɗanda za su fara a wata na bakwai a rana ta goma sha biyar, zai ba da abubuwan nan saboda hadayu don zunubi, hadayu na ƙonawa, hadayu na gari da kuma mai.
<- Ezekiyel 44Ezekiyel 46 ->