5 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ce wa Haruna, ‘Ka miƙa hannunka da sandanka bisa koguna da rafuffuka da kuma kududdufai, ka sa kwaɗi su fito su mamaye ƙasar Masar.’ ”
6 Sai Haruna ya miƙa hannunsa bisa ruwan Masar, kwaɗi kuwa suka fito, suka mamaye ƙasar Masar. 7 Amma bokaye ma suka yi abubuwan nan ta wurin sihirinsu; suka sa kwaɗi suka fito suka mamaye ƙasar Masar.
8 Fir’auna ya kira Musa da Haruna ya ce, “Yi addu’a ga Ubangiji yă ɗauke kwaɗi daga gare ni da mutanena, zan kuwa bar mutanenku su tafi su yi hadaya ga Ubangiji.”
9 Musa ya ce wa Fir’auna, “Na ba ka dama ka ba da lokacin da zan yi addu’a dominka da kuma bayinka da mutanenka, gidajenku kuwa za su rabu da kwaɗi, amma ban da waɗanda suke cikin Nilu.”
10 Fir’auna ya ce, “Gobe.”
12 Bayan Musa da Haruna sun bar Fir’auna, Sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji saboda kwaɗin da ya kawo a bisa Fir’auna. 13 Sai Ubangiji ya yi abin da Musa ya nema. Kwaɗin suka mutu a gidaje, da filaye, da kuma gonaki. 14 Aka jibga su tsibi-tsibi, ƙasar ta yi ɗoyi saboda su. 15 Amma da Fir’auna ya ga an sami sauƙi, sai ya taurare, ya ƙi yă saurari Musa da Haruna kamar dai yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.
22 “ ‘Amma zan keɓe yankin Goshen, inda mutanena suke don kada ƙudaje su taɓa wurin, domin ka sani cewa Ni, Ubangiji, ina cikin wannan ƙasa. 23 Zan sa iyaka tsakanin jama’ata da jama’arka. Gobe ne wannan mu’ujiza za tă auku.’ ”
24 Ubangiji kuwa ya yi haka. Tarin ƙuda suka zubo a fadar Fir’auna da cikin gidajen bayinsa, da ko’ina a Masar, ƙasar kuwa ta lalace saboda ƙudaje.
25 Sai Fir’auna ya kira Musa da Haruna ya ce, “Ku tafi, ku miƙa hadaya ga Allahnku, a nan a cikin ƙasar.”
26 Amma Musa ya ce, “Wannan ba zai yiwu ba. Hadayun da mukan miƙa wa Ubangiji, Allahnmu haram ne ga Masarawa. In kuwa muka miƙa hadayun da suke haram a idanunsu, ba za su jajjefe mu ba? 27 Dole mu yi tafiya kwana uku cikin hamada domin miƙa hadayu ga Ubangiji Allahnmu, yadda ya umarce mu.”
28 Fir’auna ya ce, “Zan bar ku ku tafi, don ku miƙa hadayu ga Ubangiji Allahnku, a cikin hamada, amma ba za ku tafi da nisa ba. Yanzu ku yi mini addu’a.”
29 Musa ya amsa, “Da zarar na bar ka, zan yi addu’a ga Ubangiji, gobe kuwa ƙudaje za su bar Fir’auna da fadawansa da kuma mutanensa. Sai dai a tabbata Fir’auna bai sāke yin ruɗi ta wurin ƙin barin mutane su tafi su miƙa hadayu ga Ubangiji ba.”
30 Sa’an nan Musa ya rabu da Fir’auna, ya kuma yi addu’a ga Ubangiji, 31 Ubangiji kuwa ya yi abin da Musa ya roƙa. Ƙudaje suka rabu da Fir’auna da fadawansa da kuma mutanensa; ba ƙudan da ya rage. 32 Amma a wannan lokaci ma, Fir’auna ya taurare zuciyarsa, bai kuma bar mutanen suka tafi ba.
<- Fitowa 7Fitowa 9 ->