10
Girman Mordekai
1 Sarki Zerzes ya sa a biya haraji a ko’ina a cikin daular, har zuwa ƙasashe masu nesa na bakin teku. 2 Dukan ayyukan Sarki Zerzes masu iko da masu girma tare da cikakken rahoton girmama Mordekai wanda sarki ya yi masa, ba a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Mediya da na Farisa ba? 3 Mordekai mutumin Yahuda, shi ne na biyu a matsayi bayan Sarki Zerzes, mai farin ciki kuma a cikin Yahudawa, aka kuma ɗauke shi da martaba cikin ’yan’uwansa Yahudawa. Gama ya yi aiki don kyautatawar mutanensa, ya kuma yi magana don a kyautata rayuwar dukan Yahudawa.
<- Esta 9